Ahmad Shaba: Majalisa ta amince da naɗin da Buhari ya yi a NASRDA

Ahmad Shaba: Majalisa ta amince da naɗin da Buhari ya yi a NASRDA

- Majalisar tarayya ta amince da nadin Dr Halilu Ahmad Shaba a matsayin sabon shugaban NASRDA

- Hakan ya biyo bayan tantancewa da kwamitin kimiyya da fasaha na majalisa ta yi masa bayan Shugaba Buhari ya aike da sunansa

- Dr Halilu Shaba ya karbi ragamin shugabancin hukumar ne bayan karewar wa'adin Farfesa Seidu Mohammed

Majalisar tarayya, a ranar Laraba ta tabbatar da nadin Dr Halilu Ahmad Shaba a matsayin shugaba hukumar binciken kimiyyar sararin samaniya (NASRDA).

An tabbatar da shi ne bayan duba rahoton da kwamitin majalisar ta kimiyya da fasaha ta yi yayin zaman majalisar a Abuja, The Nation ta ruwaito.

Shugaban kwamitin, Sanata Uche Ekwunife ne ya gabatar da rahoton.

DUBA WANNAN: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta tabbatar da Shaba a matsayin shugaban NASRDA
Yanzu-Yanzu: Majalisa ta tabbatar da Shaba a matsayin shugaban NASRDA. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Sanatocin sun amince a nada Shaba bayan shugaban majalisa Lawan Ahmad ya yi kuri'a a majalisar.

A ranar Talata ne shugaba Muhammadu Buhari ya mika sunan Shaba ga majalisar domin tantancewa da tabbatarwa.

Shaba ya kasance mukaddashin shugaban hukumar bayan karewar wa'adin Farfesa Seidu Mohammed a Yunin 2020.

KU KARANTA: El-Rufa'i ya umurci cocin RCCG ta cigaba da baza rassa a faɗin jihar Kaduna

A baya a ranar 2 ga watan Yulin 2019, hukumar ta sanar da nada Mr Jonathan Ungulu a matsayin mukadashin shugaba domin tabbatar da mika mulki daga tsohon shugaban zuwa sabo.

Kafin nadinsa, Shaba ya yi aiki a bangarori da dama a NASRDA inda ya jagoranci yin ayyuka daban-daban.

Kazalika, kafin nadinsa, Shaba ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaba a hukumar bada agajin gaggawa, NEMA daga 2006 zuwa 2009 kafin ya fara aiki da NASRDA.

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel