Tsohon gwamna ya fallasa shirin zagon ƙasa da ake yi wa gwamnatin Buhari

Tsohon gwamna ya fallasa shirin zagon ƙasa da ake yi wa gwamnatin Buhari

- Sanata Orji Uzor Kalu ya yi magana kan kallubalen tsaro da ke adabar Nigeria

- Dan majalisar ya ce akwai yiwuwar akwai shirin zagon kasa da ake yi wa gwamnati mai ci yanzu

- Kalu ya kuma bada shawarwari kan yadda za a yi domin magance kallubalen tsaron a kasar

Dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Tsohon gwamna ya fallasa shirin zagon kasa da ake yi wa gwamnatin Buhari
Tsohon gwamna ya fallasa shirin zagon kasa da ake yi wa gwamnatin Buhari. Hoto: OUKtweets
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Sanatan ya ce:

"Na yi imanin cewa akwai wata zagon kasa da ake yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Tugun da ake shirya masa na da yawa, ana nan ana neman yamutsa masa gwamnati da kasa.

"Ya kamata gwamnatin tarayya ta yi aiki tare da gwamnatocin jihohi. Mun yi aiki a wasu bangarorin da dama amma tsaro shine abinda ya fi muhimmanci kuma ya kamata mu magance batun, mu zo mu zauna tare."

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Arapaja ya zama sabon shugaban PDP na Kudu maso Yamma

Kalu, wanda tsohon gwamna ne ya kuma shawarci Shugaba Buhari ya kira taron tsaro da manyan hafsoshin tsaro, gwamnoni, wasu zababun tsaffin gwamnoni da tsaffin sojoji domin magance kallubalen tsaro a kasar.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel