El-Rufa'i ya umurci cocin RCCG ta cigaba da baza rassa a faɗin jihar Kaduna
- Nasiru El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya ce cocin RCCG ta cigaba da baza rasa a jihar Kaduna
- Gwamna El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban cocin RCCG na kasa, Fasto Adeboye
- Gwamnan Kadunan ya ce jihar Kaduna na bukatar addu'o'i domin shawo kan matsalolin da ta ke fuskanta don haka tana maraba da faston
Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya bukaci cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) ta cigaba da gina rasa a dukkan fadin jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.
El-Rufai ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban cocin na RCCG, Fasto Enoch Adeboye a gidan gwamnari da ke Kaduna a ranar Talata.
DUBA WANNAN: Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa
Gwamnan ya ce jihar na bukatar addu'a matuka don haka zai yi kyau cocin ta samu rassa sosai a Kaduna.
"Gwamnan ya bukaci Fasto Adeboye ya cigaba da gina rassa a jihar Kaduna domin jihar mu na bukatar addu'o'in ka, jihar mu na bukatar albarkar ka," a cewar sanarwar da tawagar watsa labaransa suka fitar bayan taron.
A cewar El-Rufai, RCCG ta kasance abin dogaro; alama ta hadin kan Nigeria da zaman lafiya da cigaba a jihar.
"Muna kuma bukatar albarka da addu'ar ka, a matsayin babban malami, domin ka taimake mu da kallubalen da muke fama da shi a nan da kasa baki daya."
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Arapaja ya zama sabon shugaban PDP na Kudu maso Yamma
Malamin addinin kiristan, wanda ya ce ya dade da sanin gwamnan tsawon shekaru. ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum mai tatausar zuciya.
Ya ce Allah ne kadai zai iya warware matsalar da ake fama da ita inda ya kara da cewa nasara na nan tafe.
A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .
Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.
Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.
Asali: Legit.ng