Shugaba Buhari ya naɗa Asabe Bashir a matsayin shugaban NCWD

Shugaba Buhari ya naɗa Asabe Bashir a matsayin shugaban NCWD

- Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Asabe Vilita Bashir a matsayin sabuwar NCWD

- Mrs Pauline Tallen, ministar harkokin mata ne ta fitar da sanarwar naɗin

- Asabe Vilita Bashir, yar asalin jihar Borno za ta kama aiki a ranar Litinin 12 ga watan Afrilu

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin Mrs Asabe Vilita Bashir a matsayin sabuwar shugaban Cibiyar Cigaban Harkokin Mata na Ƙasa, NCWD.

Ministan harkokin mata na ƙasa, Pauline Tallen ne ta fitar da sanarwar a ranar Juma'a.

Shugaba Buhari ya naɗa Asabe Bashir a matsayin shugaban NCWD
Shugaba Buhari ya naɗa Asabe Bashir a matsayin shugaban NCWD. Hoto: Daily Newstime Nigeria
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri

Sabuwar shugaban na hukumar NCWD za ta kama aiki a ranar Litinin 12 ga watan Afrilun shekarar 2021.

An haifi Asabe Vilita Bashir ne a garin Limankara da ke ƙaramar hukumar Gwoza na jihar Borno.

Ta yi karatun digirin ta na farko a bangaren nazarin lissafi da Chemistry a shekarar 1988 a jami'ar Maiduguri.

KU KARANTA: Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30

Daga bisani ta yi digirin digir-gir a ɓangaren Falsafa na koyarwa.

Kafin nadinta, Asabe Bashir ta rike mukamin yar majalisar tarayya mai wakiltar Gwoza, Chibok da Damboa a karkashin jam'iyyar All Progressives Party, APC.

Ta kuma rike kwamishinan ilimi a jihar Borno daga watan Maris na shekarar 2010 zuwa Yunin 2011. Har wa yau, ta rike mukamin kwamishinan gidaje daga Oktoban 2009 zuwa Afirilun 2010.

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel