Sheikh Khalid ya bayyana waɗanda ke asassa wutar rashin tsaro a Nigeria

Sheikh Khalid ya bayyana waɗanda ke asassa wutar rashin tsaro a Nigeria

- Babban malami Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya yi ikirarin cewa malamai da yan siyasa ne ke janyo rashin tsaro

- Sheikh Khalid ya yi wannan furucin ne wurin taron kaddamar da wani littafi da aka wallafa a birnin tarayya Abuja

- Ya ce gurbatattun mutane sune su ka kwace ragamar al'amurran addinai wadanda ke dasa kiyayya da rarrabuwan kai a zukatan mutane

A ranar Alhamis ne shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

'Yan Siyasa da Malaman Addini ne Musabbabin Rashin Tsaro, Sheikh Khalid
'Yan Siyasa da Malaman Addini ne Musabbabin Rashin Tsaro, Sheikh Khalid. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WNNAN: 'Yan bindiga sun tare ayarin motocin sojoji, sun ƙwace N28m da makamai a Benue

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Don haka ne ya yi kira ga gwamnati da ta yi gaggawar magance matsalolin Ilimi da rashin aikin yi, don a cewarsa, su ne silan rashin tsaron.

'"Bata-gari sunyi kane-kane a harkar siyasar kasar. Su ne kuma wadanda su kewa tattalin arzikin kasar wasoso kuma su ke lalata rayuwar matasa. Hakazalika, tarbiya da ilimi sun tabarbare a kasar ta yadda ko matashi ya gama karatu, babu aikin yi" In ji Khalid.

"Yanzun haka babu wani daukan hankali da karatuttukan suke yiwa matasan sakamakon rashin kula da ma'aikata ke samu daga hannun gwamnati.

"Misali, likitoci su kenan tafiya yajin aiki lokaci bayan lokaci, wanda sai an magance irin wadannan matsalolin sannan Najeriya zata samu zaman lafiya.

KU KARANTA: Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

"Har wayau, Gurbatattun mutane sune su ka kwace ragamar al'amurran addinai wadanda ke dasa kiyayya da rarrabuwan kai a zukatan mutane"

Khalid ya yi kira da gwamnati da kada ta yiwa 'yan ta'adda wata rangwame sai dai idan akwai matsanancin bukatan hakan.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel