Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri

Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri

- 'Yan bindiga sun kai hari garin Asere a kamaramr hukumar Ese-Odo jihar Ondo sun kona gidaje da dama

- Matan garin sunyi zanga-zanga kan lamarin da suke zargin wani MK ne ya kai harin

- Masu zanga-zangar sunyi ikirarin cewa ya kai musu harin ne saboda yana zargin suna tona masa asiri

- Rundunar yan sanda ta baza jami'anta a garin ta ce za ta kamo MK da yan tawagarsa su fuskanci doka

Wasu da ake zargin yan bindiga ne da ke addabar mutanen da ke zaune a bakin ruwa a karamar hukumar Ese-Odo sun kona gidaje 15 a wani hari da suka kai cikindare a garin Asere da ke gabar rafi.

The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai wa garin harin ne saboda suna zarginsu da bawa jami'an tsaro bayannan sirri kan ayyukansu.

Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri
Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Mata a garin sunyi zanga-zanga game da harin inda suka nema a kama yan kungiyar yan bindigan.

Matan masu zanga-zangan sun ce mutanen garin sun san maharan da suka fusata bayan rundunar hadin gwiwa ta JTF ta ragargaje su.

KU KARANTA: Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

Wadanda ake zargi yan kungiyar yan bindigan ne sun hada da Kutu Mone aka MK; July Mone; Best Oniwei; Iyemiyelawei Mone; Mathew Suku Polobubou; Dedewei Mone da Bado Ogbudugbudu.

Masu zanga-zangar sun ce tawagan miyagun sun dade suna cin karen su babu babbaka har zuwa lokacin da JTF ta kai musu samame.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Faith ta ce shugaban yan bindigan, Kutu Mone, dan asalin garin Asere, ya kai musu hari ne saboda yana tunanin suna bawa jami'an tsaro bayannan sirri.

KU KARANTA: Ku bada himma wurin samar da tsaro a maimakon zawarcin mu, Gwamnonin PDP ga APC

A cewarta, "Mun ga wuta na ci daga gidajen mu. Ba mu san abinda ke faruwa ba. Dukkan mu mun tsere mun shige daji a daren har sai da jami'an tsaro suka zo suka cece mu."

Kakakin yan sandan jihar, ASP Tee-Leo Ikoro ya ce: "Muna son sanar da mutanen garin nan cewa yan sanda sun dauki mataki kan lamarin. Kowa ya koma ya cigaba da harkokinsa da ya saba.

"Mun baza jami'an mu a garin kuma nan bada dadewa ba za a kama MK da yan tawagarsa a gurfanar da su."

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel