Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30

Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30

- Matar da ta fi kowa tsawon farce, Ayyana Williams ta yanke farcenta

- Hakan na zuwa ne kimanin shekaru 30 bata taba yanke farcenta ba

- Za a ajiye farcenta da aka yanke a gidan ajiye kayan tarihi na Orlando, Florida

Ayyana Williams, macen da ta kafa tarihi a matsayin wacce ta fi kowa tsawon farce a duniya ta yanke farcenta.

Williams mai zaune a garin Houston jihar Texas a Amurka ta zama mace wadda ta fi kowa tsawon farce a duniya a 2017 a lokacin da aka auna tsawonsu kimanin kafa 19.

Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30
Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30. Hoto: @GWR
Asali: Twitter

Daga karshe ta yanke farcen a karshen mako, bayan ta shafe kimanin shekaru 30 ba ta yanke su ba.

DUBA WANNAN: Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

Kafin ta yanke su, ta auna tsawonsu daga karshe inda aka gano tsawonsu kafa 24 da inci 0.7 (24 ft 0.7 in).

Tana amfani da kwalaben man farce kimanin guda hudu a tsawon awanni 20 yayin gyara farcenta kafin ta yanke su.

Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30
Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30. Hoto: @GWR
Asali: Twitter

Williams ta tafi ofishin likitocin fara a Forth Worth, Texas inda aka yi amfani da na'ura mai amfani da lantarki wurin yanke farcen da ta rika ajiyarsu tun 1990s.

"Ko da farce na ko babu su, Zan cigaba da kasancewa saurauniya," inji Williams, a cewar Guinness. "Ba farcen bane ni, ni nake da ikon barin farcen!"

Za a ajiye farcen Williams da aka yanke a gidan ajiye kayan tarihi na Orlando a Florida.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tare ayarin motocin sojoji, sun ƙwace N28m da makamai a Benue

Williams ta ce za ta bar farcenta su kai tsawon inci shida.

Saboda tsawon farcenta, Williams ba ta iya yin wasu ayyuka kamar wanke kwanuka da shimfida zanin gado.

Macen da ta fi kowa ajiye farce mai tsawo a duniya itace Lee Redmond, wacce ta fara ajiye farcenta tun 1979. Tsawonsu ya kai kafa 28 amma sun karye yayin da ta yi hatsarin mota a 2009, a cewar Guinness World Records.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel