Yanzu Yanzu: Fursunoni sama da 80 da suka tsere sun koma cibiyar gyara hali da ke Imo

Yanzu Yanzu: Fursunoni sama da 80 da suka tsere sun koma cibiyar gyara hali da ke Imo

- Akalla fursunoni 80 da suka tsere daga Cibiyar gyara hali ta Owerri ne suka dawo don radin kansu

- An tattaro cewa galibi wadanda suke jiran shari', wadanda ke da karancin zaman gidan yari da kuma wadanda ke gab da kammala wa’adinsu ne suka dawo

- Sai dai kuma wata majiya ta ce tana sa ran wasu za su dawo kafin karshen mako

Fiye da fursunoni 80 da suka tsere daga Cibiyar gyara hali ta Owerri sun dawo don radin kansu, jaridar The Nation ta ruwaito a ranar Laraba.

Wata majiya a hukumar gyara halayen ta Najeriya ta bayyana hakan ga jaridar.

Ya ce: “Kimanin 17 daga cikinsu sun dawo a ranar Talata sannan kuma a ranar Laraba, mun ga wasu sama da 20 sun dawo.

Yanzu Yanzu: Fursunoni sama da 80 da suka tsere sun koma cibiyar gyara hali da ke Imo
Yanzu Yanzu: Fursunoni sama da 80 da suka tsere sun koma cibiyar gyara hali da ke Imo Hoto: @mr_okokobioko
Asali: Twitter

"Amma galibi wadanda suke jiran shari'a ne, wadanda ke da karancin zaman gidan yari da kuma wadanda ke gab da kammala wa’adinsu, sun dawo ya zuwa yanzu".

KU KARANTA KUMA: Lokacin da kudinmu ke da daraja: Yan Najeriya yi zazzafan martani yayin da hotunan tsoffin naira suka bayyana

Kimanin fursunoni 42 suka dawo a yammacin ranar Litinin, wanda ya dauki jimillan wadanda suka dawo zuwa 80.

“Matsalar da muke fama da ita, kuma bai da nasaba da fasa gidan yarin nan, shine babu wani daga cikin fursunoni masu manyan laifuka da suka tsere da suka dawo.

"Wannan abin fahimta ne saboda zai yi wuya ga mutumin da ya san cewa za a iya yanke masa hukuncin a kowane lokaci, ya dawo bayan wadanda suka kutsa cikin cibiyar sun ba shi 'yancinsa kyauta," in ji majiyar.

Wasu ‘yan bindiga da‘ yan sanda suka ce ’yan kungiyar IPOB ne sun kai hari a gidan yari tare da‘ yanta fursunoni 1,844 a ranar Litinin.

Ana tsammacin hakan tare da afuwar da Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar, yawancin wadanda suka tsere za su koma gidan don ci gaba da wa’adinsu.

KU KARANTA KUMA: Mallam dogo: Baiwar tsayi da Allah yayi wa wani saurayi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya

Majiyar ta kara da cewa:

“Yawancin fursunonin da suka dawo sun samu rakiyar iyayensu, lauyoyi da danginsu.

“Muna sa ran wasu za su dawo nan da karshen mako.”

A wani labarin, wasu yan bindiga sun sake bankawa ofishin yan sanda wuta a jihar Imo, yan awanni bayan ziyarar da mataimakin shugaban kasa da Sifeto Janar na yan sanda, IGP Adamu suka kai ziyara jihar.

Tafiyar Osinbaji ke da wuya, yan bindigan suka banka wuta hedkwatar yans andan karamar hukumar Ehime Mbano.

The Nation ta tattaro cewa suna dira ofishin yan sandan suka kubutar da dukkan wadanda ke tsare sannan suka banka wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel