Mallam dogo: Baiwar tsayi da Allah yayi wa wani saurayi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya

Mallam dogo: Baiwar tsayi da Allah yayi wa wani saurayi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya

- Wani bawan Allah ya haifar da gagarumin cece-kuce a shafukan sada zumunta saboda yanayin surar da Allah yayi masa

- Dan Najeriyan ya wallafa hotunan wani bikin aure da ya halarta kwanan nan amma sai tsayinsa ya dauki hankulan mutane da yawa

- Yayin da wasu ke cewa ya sa duk wadanda ke kusa da shi sun zama gajeru, wasu kuma sun bayyana cewa ba za su iya daukar hoto tare da shi ba

Wani dan Najeriyar da Allah ya azurta shi da tsayi sosai ya haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kamar yadda koda mutum na da tsayi idan ya tsaya kusa da shi sai ya gajarce.

An yi wannan cece-kucen ne a shafin Twitter bayan @alameengimba ya wallafa hotunansa tare da bakin da suka halarci bikin da ya halarta.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya gina gidaje 500 ga 'yan gudun hijira a Nguro Soye

Ya rubuta:

"Bakon bikin aure ... Ina son daukar hotuna da gajerun mutane."

@alameengimba na da tsayin da ya kai sahu shida da inci takwas.

Wallafar tasa ta samu gagarumin martani tare da ‘likes’ fiye da dubu 7 a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Tsayinsa ya tsorata mutane da yawa inda suka ce ba za su taba yi masa tayi ko amsa tayin daukar hoto tare da shi ba.

Mallam dogo: Baiwar tsayi da Allah yayi wa wani saurayi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya
Mallam dogo: Baiwar tsayi da Allah yayi wa wani saurayi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya Hoto: @alameengimba
Asali: Twitter

@sopzeeworld tayi martani:

"Mahaifiyata ta taba fada min cewa cin wake na iya sa mutum ya kara tsayi. Wa ya san buhun wake nawa wannan mutumin ya ci."

@earhmerd ya ce:

"Tambayata a nan ita ce idan kana son sumbatar abokiyar zamanka a tsaye, yaya abin zai kasance?"

@FolasadeOlukoju ya ce:

"Ina mamakin yadda kake lanƙwasa don shiga mota da kuma yadda za ka lanƙwasa yayin tuka ta."

KU KARANTA KUMA: Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sandan da ya shiga yi wa sata

@ sadiqshettima89 ya yi tsokaci:

"Shin kana da tsayi ne sosai ko kuma mutanen da ke kusa da kai ne gajeru? Ina taya kanwata tambaya ne."

A wani labarin, Babangida Sadiq Adamu, mutumin da ya auri mata biyu a rana daya ya bayyana yadda rayuwar aurensu take tafiya.

Dama labarinsa ya watsu a kafafen sada zumunta inda kowa ya tofa albarkacin bakinsa.

A wata tattaunawa da BBC Pidgin suka yi dashi ya bayyana yadda yake samun nishadi tun da ya auri mata biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel