Yanzu-yanzu: Wasu yan bindiga sun sake banka wuta ofishin yan sanda a Imo

Yanzu-yanzu: Wasu yan bindiga sun sake banka wuta ofishin yan sanda a Imo

Wasu yan bindiga sun sake bankawa ofishin yan sanda wuta a jihar Imo, yan awanni bayan ziyarar da mataimakin shugaban kasa da Sifeto Janar na yan sanda, IGP Adamu suka kai ziyara jihar.

Tafiyar Osinbaji ke da wuya, yan bindigan suka banka wuta hedkwatar yans andan karamar hukumar Ehime Mbano.

The Nation ta tattaro cewa suna dira ofishin yan sandan suka kubutar da dukkan wadanda ke tsare sannan suka banka wuta.

Hakazalika an samu labarin cewa sun gudanar da hakan ba tare da wani ya yi yunkurin dakatad da su ba.

Wata majiya tace: "Yan bindiga da yamman nan sun kona hedkwatar yan sanda na karamar hukumar Ehime Mbano. Daga isarsu, sun kubutar da wadanda ke tsare kafin aika-aikan da suka yi."

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu, ya bayyana cewa bai samu labarin harin ba. Amma wani babban jami'in dan sanda wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa hukumar bata ji dadin wannan sabon harin ba.

Yanzu-yanzu: Wasu yan bindiga sun sake banka wuta ofishin yan sanda a Imo
Yanzu-yanzu: Wasu yan bindiga sun sake banka wuta ofishin yan sanda a Imo
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng