Lokacin da kudinmu ke da daraja: Yan Najeriya yi zazzafan martani yayin da hotunan tsoffin naira suka bayyana

Lokacin da kudinmu ke da daraja: Yan Najeriya yi zazzafan martani yayin da hotunan tsoffin naira suka bayyana

- Yan Najeriya sun tuna baya bayan an wallafa hotunan tsoffin naira a shafin soshiyal midiya

- Mutane sun ce sun yi kewar zamanin da kudin Najeriya ke da daraja bayan wani mai amfani da Twitter ya wallafa hotunan kudi na naira 20 da 50

- Wasu daga cikin wadanda suka yi tsokaci a kan wallafar sun ce har yanzu iyayensu na nan da kudaden

Hotunan tsoffin kudin Najeriya sun bayyana kwanan nan a shafukan sada zumunta kuma hakan ya sa mutanen kasar tunawa da zamanin baya.

Shafin @NigeriaStories ya wallafa hotunan kudi na naira 20 da 50 kuma ya nemi masu amfani da Twitter da su sake yada rubutu idan sun tuna ko sun yi amfani da su.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya gina gidaje 500 ga 'yan gudun hijira a Nguro Soye

Lokacin da kudinmu ke da daraja: Yan Najeriya yi zazzafan martani yayin da hotunan tsoffin naira suka bayyana
Lokacin da kudinmu ke da daraja: Yan Najeriya yi zazzafan martani yayin da hotunan tsoffin naira suka bayyana Hoto: @NigeriaStories
Asali: Twitter

Ba da daɗewa ba 'yan Najeriya suka mamaye ɓangaren sharhi na rubutun don bayyana ra'ayinsu kan lamarin.

Wani mai amfani da Twitter @SirLewis93 ya ce har yanzu mahaifiyarsa tana da takardun N20, ya kara da cewa ba ta san dalilin da yas har yanzu take ajiyarsu ba.

A kalamansa:

"Har yanzu mahaifiyata tana da tarin tsofaffin kudi na 20NGN. Har yanzu ban san dalilin da ya sa take ajje su ba."

Ubong Francis tare da shafin Twitter @ Ubongfrancis1 ya ce an kashe kudaden ne lokacin da kudin Najeriya ke da daraja.

@Ubongfrancis1 ya ce:

"Lokacin da kuɗinmu suka kasance masu daraja."

@Nwanyi_maramma yayi sharhi:

"Shekaru 3 da suka gabata na gan su da yawa a ƙarƙashin akwatin mahaifiyata. Kimanin 5000naira gaba ɗaya. Waɗannan kudi masu daraja ne."

KU KARANTA KUMA: Ta bayyana: Rigingimu 3 da suka tilastawa Shugaba Buhari tsige IGP Adamu

@ACealaowei21 ya rubuta:

"Lokacin da Naira ke da Daraja."

A wani labarin, wani dan Najeriyar da Allah ya azurta shi da tsayi sosai ya haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kamar yadda koda mutum na da tsayi idan ya tsaya kusa da shi sai ya gajarce.

An yi wannan cece-kucen ne a shafin Twitter bayan @alameengimba ya wallafa hotunansa tare da bakin da suka halarci bikin da ya halarta.

@alameengimba na da tsayin da ya kai sahu shida da inci takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel