Yan Bindiga sun hallaka Ma'aikata Biyu a makarantar Poly Dake Jihar Zamfara

Yan Bindiga sun hallaka Ma'aikata Biyu a makarantar Poly Dake Jihar Zamfara

- Wasu yan bindiga sun hallaka ma'aikata biyu a makarantar Poli dake Ƙauran-Namoda, jihar Zamfara

- 'Yan bindigar sun ɓude wuta ga ma'aikatan biyu, Usama Nazifi da Bashiru Muhammed ya yin da suke tsakar tattaunawa.

- Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar ya bayyana cewa kwamishina ya ɗauki matakin gaggawa wajen tura jam'ai na musamman yankin don su gudanar da bincike

Rundunar yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da kisan Usama Nazifi da Bashiru Muhammed, dukkan su ma'aikata ne a makarantar poli mallakar gwamnatin tarayya dake Ƙauran-Namoda.

KARANTA ANAN: Kishi kumallon mata: Uwargida ta kashe kishiyarta sannan ta kona gawarta

SP Mohammed Shehu, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ya tabbatar a aukuwar lamarin a wani saƙo da ya aike ma manema labari a Gusau, babban birnin Zamfara.

A bayanin da yayi, yace yan bindigar sun je gidan ɗaya daga cikin ma'aikatan Usama Nazif, suka nemi ya ɓuɗe musu ƙofa.

Ya yin da Nazifi ya fara kira da karfi don neman taimako sai maharan suka gudu suka ɓuya a jikin gidajen dake mƙwabtaka da gidan Nazifi.

Wani shaida ya bayyana cewa a dai-dai wannan lokacine ne, kofar gidan dake maƙwaftaka dashi ta buɗe, Bashiru Muhammed ya fito yazo gidan Nazifi don yaga meke faruwa.

Yan Bindiga sun hallaka Ma'aikata Biyu a makarantar Poli Dake Jihar Zamfara
Yan Bindiga sun hallaka Ma'aikata Biyu a makarantar Poli Dake Jihar Zamfara Hoto: @Daily_trust
Source: Twitter

Shaidar ya cigaba da cewa, sai kawai yan bindigar suka fito ba zato ba tsammani lokacin da Usama Nazifi da Bashiru Muhammad suke tattaunawa akan lamarin.

KARANTA ANAN: 2023: Gwamnonin Kudu maso Yamma na neman janyo wa Tinubu matsala, Miyetti Allah

Yan bindigar basuyi wata-wata ba sai suka buɗe musu wuta, suka kashe mutanen biyu nan take, kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

A halin yanzu, mai magana da yawun hukumar 'yan sanda yace kwamishinan yan sandan jihar, Mr Abutu Yaro, ya aike da jami'ai na musamman don subi sawun maharan su kamo su.

Sai dai, mai magana da yawun 'yan sandan ya yi kira ga mutanen yankin su taimaka su bada sahihiyar masaniya da zata taimaka ma jami'an kamo masu laifin.

A wani labarin kuma ‘Yan sanda sun cafke wani mai POS wanda ke taimakawa masu satar mutane wajen karbar kudin fansa

An kama wani mai POS, Gadimoh Ofei Bright, akan wani lamari da ke da nasaba da satar mutane a jihar Edo.

Bright ya tona cewa ya kan taimaka wa masu satar mutane wajen karbar kudin fansa daga dangin wadanda suke sacewa.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Source: Legit

Online view pixel