Kishi kumallon mata: Uwargida ta kashe kishiyarta sannan ta kona gawarta

Kishi kumallon mata: Uwargida ta kashe kishiyarta sannan ta kona gawarta

- Uwargida ta lakadawa kishiyarta dukan tsiya har lahira sannan ta kona gawarta

- An kashe amaryar mai suna Fatima wacce ke a Sabuwar Unguwa, garin Katsina watanni biyu da yin aurenta

- Lamarin ya afku ne a ranar Talata, 23 ga watan Maris

Rahotanni sun kawo cewa wata mata ta lakadawa kishiyarta dukan tsiya sannan ta cinnawa gawarta wuta.

Kishiyar mai suna Fatima daga yankin Sabuwar Unguwa, garin Katsina, ta yi aure kimanin watanni biyu da suka gabata, jaridar Dateline ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Na shirya: Budurwa ta tsayar da ranar da za a daura aurenta ba tare da miji ba, ta buga katin gayyata

Kishi kumallon mata: Uwargida ta kashe kishiyarta sannan ta kona gawarta
Kishi kumallon mata: Uwargida ta kashe kishiyarta sannan ta kona gawarta Hoto: Dateline
Asali: UGC

A cewar wata majiya ta kusa da iyalan, lamarin ya afku ne a ranar Talata tana mai cewa, “na ji cewa matar ta je gidan Fatima tare da mutum daya ko biyu.

“Shakka babu ba da niyan kasheta suka yi ba, amma da suka ga cewa bata numfashi bayan sun yi mata duka, sai suka cinnawa dakinta da gawarta wuta.

“Mahaifin Fatima, Mallam Ibrahim, wanda ke karantarwa a wata makarantar Islamiyyah da ke gidan AIG Umar Maiwada ya shiga dimuwa da ya samu labarin.

“An shirya yin jana’izar marigayiya Fatima a ranar Laraba a Sabuwar Unguwa.”

KU KARANTA KUMA: Manyan kasashe 17 mafi farin ciki a Afirka a 2021, Najeriya ce ta karshe

Zuwa yanzu babu cikakken bayani daga rundunar yan sandan jihar.

Har ila yau shafin Instagram mai suna northern_hibiscuss ya wallafa labarin kisan inda mutane suka tofa albarkacin bakunansu.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin a kasa:

mobilhumaira ta ce:

"Wllh da gaske ne a Nan kt abun ya faru ko gawar ba a rufe ba, sai gobe da safe in Allah ya kaimu just two months da yin auren Allah ya jikan Fatima."

Wani mai suna dare_to_dazzle_by_fdl ya yi martani cewa:

"Allah Ya shirya mu Ya tsare mu daga mummunar kaddara amin, Ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu amin, this is so unfortunate wllhi, Mata wllhi muji tsoron Allah mace fa Bata auren Kanta Sai an auro ta wllhi idan baa fara daukan mataki Akan irin wannan masifar ba wllhi Baza a zauna lfy ba wllhi."

bakatsina_19 ta ce:

"Allah ya jikanta da rahama Nima irin abunda akaso ayimun kenan tawa shigowa tayi but I try to fight her back ban yadda tayimun nikis bah ama Alhamdulillahi an shigo an rabamu malama imagin akaina mijinmu ya dau Mataki he divorce me instead of her ita datazo her cikin gidana ta buge ni ama ba abunda yayi Mata insha Allah YUNUSA & iklima karshanku bazai taba kyauba Allah ya sakamun abunda kuka Mani rayuwata."

khady_harun ta ce:

"Allah ubangiji ya jinkan ta mu kuma yasa mufi karfin zuceyoyinmu ya rabamu da aikin da nasani ameen thmmah ameen "

A gefe guda, mun ji cewa akalla mutane biyu aka kashe sannan aka sace guda a wani sabon harin a aka kai a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara, TVC News ta ruwaito.

Wadanda aka kashe ma'aikata ne a Kwallejin Fasaha ta Kaura Namoda.

Wasu da ake zargin yan bindiga ne suka kashe su a safiyar ranar Laraba.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel