‘Yan sanda sun cafke wani mai POS wanda ke taimakawa masu satar mutane wajen karbar kudin fansa
- An kama wani mai POS, Gadimoh Ofei Bright, akan wani lamari da ke da nasaba da satar mutane a jihar Edo
- Bright ya tona cewa ya kan taimaka wa masu satar mutane wajen karbar kudin fansa daga dangin wadanda suke sacewa
- A kan lamarin wanda ake gudanar da bincike a kai, mai POS din ya taimaka wa masu garkuwan wajen karbar kudi sama da miliyan daya daga dangin wadanda aka sacen
Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo ta cafke wani mai POS wanda ake zargi da taimakawa ‘yan fashi da makami da masu satar mutane wajen karbar kudi daga asusun bankunan wadanda lamarin ya cika da su.
An kama dan shekara 29 din mai suna Gadimoh Ofei Bright 29 a ranar Talata, 23 ga Maris, a Igarra da ke karamar hukumar Akoko-Edo bayan bincike na musamman ta hanyar bayanan sirri kan wani lamari na garkuwa da mutane, PM News ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Dan Allah ka farka, kasar nan na wargajewa - Baba Ahmed ga Buhari
Legit.ng ta tattaro cewa a kan lamarin da ake gudanar da bincike, an sace mutane da dama tare da yin fashi a yankin Ugbowo da ke cikin garin Benin.
An tura kudi daga asusun ajiyar wadanda abun ya cika da su a matsayin kudin fansa zuwa wani asusun banki kafin aka sake su.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar yan sandan, SP Kontongs Bello, ya nuna cewa mai POS da aka kama ya furta cewa ya taimaka wa ’yan fashi wajen karbar kudi daga wadanda suka sace.
Ya ce ya karɓi kuɗin N1, 130,000 a cikin lamarin da ake bincike a kai daga dangin wanda abin ya shafa kafin aka sake shi.
KU KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Kaduna, Sun Kashe Huɗu Sun Raunta Wasu
Kayayyakin da aka kwato daga wurinsa sun hada da na’urorin POS guda biyu, katunan ATM guda 11 dauke da sunaye daban-daban, wayoyin hannu biyar da katinan SIM da kuma kudi N156,000.
A wani labarin, wasu yan bindiga sun farmaki yan sanda ya yin da suke sintiri a garin Ashaka, karamar hukumar Ndokwa ta gabas a jihar Delta.
Yan bindigan sun caka ma ɗaya daga cikin yan sandan wuƙa wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa kuma suka jikkata wasu sannan suka babbaka ma motar da yan sandan ke sintiri da ita wuta.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa maharan sun kori 'yan sandan da tsiya kuma suka yi gaba da makaman su.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng