2023: Gwamnonin Kudu maso Yamma na neman janyo wa Tinubu matsala, Miyetti Allah

2023: Gwamnonin Kudu maso Yamma na neman janyo wa Tinubu matsala, Miyetti Allah

- Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta ce gwamnonin kudu maso yamma ne neman kawo wa takarar shugabancin kasa na Tinubu matsala

- Mai magana da yawun kungiyar, Allah Saleh Alhassan ne ya bayyana hakan yayin wata hirar da aka yi da shi

- Alhassan ya ce idan Tinubu ya matsa da magana kan rikicin makiyaya zai iya rasa samun goyon bayan mutanen da abinda ya fada bai musu dadi ba

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Horre ta ce gwamnonin jihohin kudu maso yamma, da ke korar makiyaya daga jihohinsu na janyo wa Bola Tinubu matsala game dangane da hasashen da ake yi na cewa yana son yin takarar shugaban kasa a 2023.

Kakakin Miyetti Allah, Saleh Alhassan ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi da shi a ranar Laraba a shirin 'The Roundtable' na Punch Online.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

2023: Gwamnonin Kudu maso Yamma ne neman janyo wa Tinubu matsala, Miyetti Allah
2023: Gwamnonin Kudu maso Yamma ne neman janyo wa Tinubu matsala, Miyetti Allah. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A baya-bayan nan an rika zargin makiyaya musamman a yankunan kudu maso yamma da laifukan afkawa gonakin manoma suna cinye amfanin da shanunsu da kuma aikata laifuka irinsu garkuwa da mutane da kashe kashe.

Gwamnonin jihohin kudu karkashin kungiyarsu da gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ke yi wa jagoranci sun bullo da hanyoyin magance matsalar da suka hada da hana kiwo a fili, kiwon dare, hana kananan yara kiwo da sauransu.

DUBA WANNAN: Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

Shugabannin Yarbawa da dama irinsu Cif Ayo Adebanjo na Afenifere ya ce Tinubu na tsoron yin magana game da batun rikicin makiyaya saboda kada abin ya janyo masa matsala a takarar shugaban kasa a 2023 kuma don baya son bata wa Shugaba Muhammadu Buhari rai.

Amma tsohon gwamnan na Legas ya yi magana game da rikicin makiyayan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 13 ga watan Maris mai lakabin 'Jawabin Tinubu game da rikicin makiyaya da manoma'.

A cikin jawabin, Tinubu ya shawarci gwamnonin kudu su sauya filayen gwamnati da ba a amfani da su zuwa filayen kiwo na makiyaya.

A martaninsa, kakakin na Miyetti Allah ya yabawa matsayan na Tinubu amma ya ce kasar ba ta shirya aiwatar da shawarwarin magance matsalar ba.

Alhassan ya ce, "Na tausayawa Tinubu domin idan ya kara fadin wani abu fiye da abinda ya fada, za su ce yana neman takarar shugaban kasa ne. Shi yasa ya dade kafin ya yi magana amma ina tsamanin zai kira yaransa na siyasa - wadanda suke gwamnoni - da ke kawo wannan rudanin. Ya kira su ya ce, 'Idan na zama shugaban kasa, zan magance mana wannan matsalar kuma ba zan haifar masa matsala."

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel