Kuɗin Makamai: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Gwamnan CBN da kuma COAS da Suzo Su Mata Bayani

Kuɗin Makamai: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Gwamnan CBN da kuma COAS da Suzo Su Mata Bayani

- Kwamitin da majalisar wakilai ta kafa ɗon binciko yadda aka siyo makamai a ƙasar nan ya aike da gayyata ga shugaban sojoji (CAS), da kuma gwamnan babban bankin Najeria.

- Majalisar ta kafa kwamitin ne domin duba yadda aka siyo kuma aka yi amfani da makamai a ƙasar nan

- Sauran waɗanda aka aike ma da gayyata sun haɗa da ma'aikatar kuɗi, ma'aikatar tsaro, da kuma ma'aikatar harkokin cikin gida.

'Yan majalisar wakilan ƙasar nan sun kirayi gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, da kuma shugaban rundunar sojojin ƙasar nan, Mejo Janar Ibrahim Attahiru, su bayyana a gaban ta domin su amsa tambayoyi akan yadda aka yi amfani da kudin makamai.

KARANTA ANAN: 2023: Zan 'Raba Jiha' Da Jonathan Muddin Ya Ce Zai Yi Takara a APC, Wike

An ɗauki matakin ne a taron da kwamitin wucin gadi da majalisar ta kafa don buƙatar sake duba yadda aka siyo kuma akayi amfani da makamai da sauran kayayyakin yaki na jami'an tsaro, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Gaayyatar ta umarci manyan mutanen biyu su bayyana a gaban majalisar ranar bakwai ga watan Afrilu da misalin karfe biyu na yamma.

Kuɗin Makamai: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Gwamnan CBN Da kuma COAS Da Suzo Su Mata Bayani
Kuɗin Makamai: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Gwamnan CBN Da kuma COAS Da Suzo Su Mata Bayani Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Sauran waɗanda majalisar ta aike ma da gayyatar sun haɗa da, ma'aikatar kuɗi, ma'aikatar tsaro, da kuma ma'aikatar harkokin cikin gida.

KARANTA ANAN: Yadda Ƴan Banga Suka Yi Fito-Na-Fito da Masu Garkuwa a Abuja

Shugaban Sojojin ƙasar nan ya tura wakilinshi, mejo janar C. Ofuche, a ya yin zaman majalisar na baya-bayannan, amma majalisar tace bata yarda ba sai dai yazo da kansa.

Mambobin kwamitin sun bayyana cewa lamarin na buƙatar ganin shugaban da kansa.

A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Cafke Gungun Masu Garkuwa da Mutane A Adamawa

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta bayyana nasarar cafke wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen satar mutane da kuma fashi da makami a jihar.

Ana zargin mutanen da hana al'umma sakat a bodar data haɗa Najeriya da ƙasar Kamaru.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Source: Legit

Online view pixel