2023: Zan 'Raba Jiha' Da Jonathan Muddin Ya Ce Zai Yi Takara a APC, Wike
- Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ba zai goyi bayan Goodluck Jonathan ba idan ya yi takarar shugaban kasa a APC
- Wike ya ce duk da cewa dukkansu mutanen kudu ne, ba zai taba iya juyawa jam'iyyarsa ta PDP baya ba domin kabilanci
- Wike ya kuma soki Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, saboda kiransa ma'aikacinsa inda ya ce ta dalilinsa ne Amaechi ya zama gwamna
Gwamnan Rivers, Nyesome Wike ya ce ba zai mara wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan baya ba ko da ya samu tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2023, rahoton The Nation.
A hirar da ya yi da BBC Pidgin a karshen mako a Port Harcourt, gwamnan ya kuma ce Allah ya yi amfani da shi wurin nada Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, zama gwamnan Rivers.
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: An Kai Hari Gidan Mahaifiyar Sunday Igboho
Wike ya ce ko shi Jonathan ya ce cewa shi (Wike) zan juya masa baya idan ya shiga APC ya kuma samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar a zaben 2023.
Ya ce: "Ni dan PDP ne, Idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyya ta, zan mara masa baya. Amma idan ya samu tikitin a APC, ba zan goyi bayansa ba domin ba zan ci amanar jam'iyya ta ba.
"Ya san cewa ba zan mara masa baya ba a APC duk da cewa daga Kudu ya fito. Bana irin wannan siyasar. Jam'iyya muke magana ba kabilanci ba."
KU KARANTA: Matar Da Za Ta Auri Sojan Saman Da Aka Kashe a Kaduna Ta Auri Yayansa
Wike ya kuma soki Amaechi saboda kiransa ma'aikacinsa inda ya ce Ministan Sufurin ya zama gwamnan jihar Rivers ne saboda Allah ya yi amfani da shi (Wike) a matsayin sanadi ba.
A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.
Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.
Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng