Yadda Ƴan Banga Suka Yi Fito-Na-Fito da Masu Garkuwa a Abuja

Yadda Ƴan Banga Suka Yi Fito-Na-Fito da Masu Garkuwa a Abuja

- Yan banga sun fattaki masu garkuwa da mutane a garin Kekeshi a Abuja

- Yan bindigan sunyi niyyar afkawa garin ne a daren ranar Juma'a amma ba su yi nasara ba

- Ɗaya daga cikin yan bangan da ya fita fitsari ne ya ankarar da yan uwansa suka fattaki yan bindigan

Yan banga sun dakile harin da wasu da ake zargi masu garkuwa ne suka kai a garin Kekeshi a ƙaramar hukumar Abaji a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

An sace mutum hudu a garin ciki har da wani yaro mai shekaru 14 kuma har yanzu ba a sako su ba, masu garkuwar na neman Naira miliyan 10.

Yadda Ƴan Banga Suka Fatattaki Masu Garkuwa a Wani Garin Abuja
Yadda Ƴan Banga Suka Fatattaki Masu Garkuwa a Wani Garin Abuja. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Matar Da Za Ta Auri Sojan Saman Da Aka Kashe a Kaduna Ta Auri Yayansa

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakayya sunansa ya ce lamarin ya faru a ranar Juma'a da ta gabata da dare misalin ƙarfe 9.22 na dare.

An ruwaito cewa wasu da ake zargi masu garkuwa ne sunyi yunkurin sace wasu mutane a gidajen da ke wajen garin.

Ya ce wani ɗan banga a garin ya tafi yin fitsari ne sai ya hangi hasken fitila daga nesa.

"Daya daga cikin yan banga da ke zaune a nan ya tafi fitsari a bayan gida sai ya hango hasken fitila, shima sai ya haska fitilar sa," in ji shi.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: An Kai Hari Gidan Mahaifiyar Sunday Igboho

Ya ce daya daga cikin masu garkuwar ya harbi bindiga a iska bayan ganin hasken fitilarsa hakan yasa sauran yan bangan suka fara harba nasu bindigan.

Ya ce harbin da yan bangan suka yi ne yasa masu garkuwar suka tsere.

"Yan bangan sun yi musayar wuta da su har zuwa wani kududufi a wajen garin har sai da suka tsere," in ji shi.

Kakakin yan sandan birnin tarayya Abuja, ASP Maryam Yusuf bata amsa sakon text ɗin da aka aike mata ba game da afkuwar lamarin.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit

Tags:
Online view pixel