'Yan Sanda Sun Cafke Gungun Masu Garkuwa da Mutane A Adamawa

'Yan Sanda Sun Cafke Gungun Masu Garkuwa da Mutane A Adamawa

- Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta bayyana nasarar cafke wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen satar mutane da kuma fashi da makami a jihar.

- Ana zargin mutanen da hana al'umma sakat a bodar data haɗa Najeriya da ƙasar Kamaru

- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya jinjina ma ƙoƙarin jami'an sa kuma ya basu umarnin su cigaba da bincike dan kamo duk wanda ake zargi.

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa sun samu nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu wajen sace wani injiniya, da shugaban masu kula da wurin bada horon jihar dake Jabbi Lamba.

KARANTA ANAN: Dole in binciki satar N30bn a kwangilar ruwan da Oshiomhole su ka yi inji Gwamna Obaseki

'Yan sandan sun kuma cafke wasu mutane biyu da ake zargin yan garkuwa ne, Alhaji Jauro Mamburso da kuma Alkani Zumbe.

Sun gano cewa Alhaji Jauro Manburso ɗan ƙaramar hukumar Girei ne, yayinda Alkani Zumbe ya fito daga ƙaramar hukumar Song dake jihar ta Adamawa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya ce rundunar ta samu nasarar ƙwato bindigu daga hannun mutane ukun da suka cafke, mutanen sune, Usman Sale, Lawwali Sale da kuma Yerima dadi.

'Yan Sanda Sun Cafke Gungun Masu Garkuwa da Mutane A Adamawa
'Yan Sanda Sun Cafke Gungun Masu Garkuwa da Mutane A Adamawa Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Nguruje ya bayyana haka ne yayinda aka shigar da mutum ukun da ake zargi hedkwatar rundunar yan sandan ta jihar ranar Asabar.

KARANTA ANAN: Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi hakan

Ya ƙara da cewa sun kama waɗanda ake zargin a maɓoyarsu dake ƙauyen Muleng da Chigari ƙaramar hukumar Song, ya kuma bayyana cewa yan sanda sun tsananta bincike ne bayan samun wata masaniya akan waɗanda ake zargin tare da haɗin gwuiwar jami'an sa kai na karamar hukumar Song.

Bayan gudanar da bincike 'yan sanda sun gano cewa waɗanda aka kama suna da hannu wajen satar mutane da fashi da makami a bodar da ta haɗa Najeriya da ƙasar Kamaru.

Sa'ilin da yake jawabin kan nasarar da suka samu, kwamishinan 'yan sandan jihar Adamawa, Aliyu Adamu, ya bawa jami'an sa umarnin cigaba da bincike dan gano sauran ƴan uwansu da kuma samo kwararan shaidu don mika su gaban kotu.

Ya kuma jinjina ma ƙoƙarin da jami'ansa keyi wajen yaƙi da laifuka a jihar, ya ƙara da cewa su cigaba da bincike kuma su yi amfani da duk wata masaniya da suka samu ta hanyar da ya dace.

A wani labarin kuma 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

Sojojin Kamaru biyu da aka tura zuwa Najeriya sun mutu da yammacin ranar Asabar a wani harin Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Majiya daga sojojin Najeriya sun tabbatar da faruwar lamarin a wani yankin jihar Borno.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Online view pixel