Buhari Ya Sanya ma wata hanya a Abuja Sunan Shugaban ƙasar Nijar

Buhari Ya Sanya ma wata hanya a Abuja Sunan Shugaban ƙasar Nijar

- Shugaban Kasa Buhari ya raɗa ma wata sabuwar hanya a Abuja sunan shugaban Kasar Nijar Mahamadou Issoufou.

- Ministan Abuja, Muhammad Bello, ya sanar da haka ya yin kaddamar da hanyar jiya Talata a babban birnin tarayya.

- An ruwaito cewa Shima Shugaban Nijar ɗin ya bama shugaba Buhari kyauta mafi kololuwa a Nijar.

Shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya raɗa wa wata sabuwar hanya a Abuja sunan takwaransa, shugaban ƙasar Nijar, Mahamadou Issoufou.

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello, tare da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya sanar da haka a ranar Talata yayin da ake ƙaddamar da hanyar.

KARANTA ANAN: 2023: Ana halin fargaba yayinda PDP ke shirin yanke hukunci kan yankin da za ta baiwa tikitin Shugaban kasa

Ministan Abuja, Muhammad Bello, ya bayyana cewa:

"Da safiyar yau, an raɗa ma babbar hanyar fita Abuja ta kudu sunan shugaban ƙasar Nijar 'Mahamadou Issoufou Expressway’ domin nuna giramamawa ga shugaban."

"Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya ma hanyar sunan takwaran nasa ne don nuna tsantsar godiyarsa da kuma ƙara dankon zumuncin dake tsakanin Najeriya da jamhuriyar Nijar, da kuma ƙara bayyanar da rawar da Shugaban ƙasa Buhari ke takawa wajen inganta zaman lafiya a Africa baki ɗaya." inji ministan.

Buhari Ya Sanya ma wata hanya a Abuja Sunan Shugaban ƙasar Nijar
Buhari Ya Sanya ma wata hanya a Abuja Sunan Shugaban ƙasar Nijar Hoto@BashirAhmad
Asali: Twitter

Domin nuna tsantsar farin cikinsa da wannan girmamawar, shugaban ya rubuta a shafinsa na twitter:

"Ɗan uwa kuma abokina shugaba Buhari, ya girmamani da kiran hanya a Abuja ‘Mahamadou Issoufou Expressway’. Wannan na ƙara nuni da kyakkywar alaƙar dake tsakanin Najeriya da Nijar ta zarce tunanin me tunani. Wannan kulawar da ya nuna min ta matukar taɓa ni. Nagode sosai."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Danbarwa ta ɓarke a majalisar dattijai kan Kudirin samar da Hukumar kula da Jami'an tsaro

Da yawan 'yan Najeriya na ganin akwai alamar tambaya a wannan dangantaka dake tsakanin shugabannin biyu.

Musamman ganin yadda Najeria ta bada kwangilar $1.959Biliyan don gina hanyar jirgin ƙasa daga jihar Kano zuwa Maraɗi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a jiya Talata takwaran nasa na jamhuriyar Nijar ya ba Shugaba Buhari kyauta mafi ƙololuwa a Nijar 'Grand Croix Des Ordre National Du Niger'.

A wani labarin kuma An samu rudani a Kaduna yayinda El-Rufai da ma’aikata suka ba da umarni daban-daban kan rufe makarantu

Yayinda Gwamna El-Rufai yace jihar ba za ta rufe makarantu ba saboda rashin tsaro, ma'aikatar ilimi kuma ta yi umurnin rufe makarantu a karamar hukumar Kajuru

Hakan ya sanya rudani a tsakanin mutane na rasa sanin umurnin wanda za su bi.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel