An samu rudani a Kaduna yayinda El-Rufai da ma’aikata suka ba da umarni daban-daban kan rufe makarantu
- An samu rabuwar kai tsakanin gwamnan jihar Kaduna da ma'aikatar ilimi ta jihar
- Yayinda Gwamna El-Rufai yace jihar ba za ta rufe makarantu ba saboda rashin tsaro, ma'aikatar ilimi kuma ta yi umurnin rufe makarantu a karamar hukumar Kajuru
- Hakan ya sanya rudani a tsakanin mutane na rasa sanin umurnin wanda za su bi
An samu rudani game da matsayin makarantu a karamar hukumar Kajuru biyo bayan sanarwar da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi cewa dukkan makarantun jihar su kasance a bude.
Sai dai kuma, wata wasika daga Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta umarci a rufe dukkan makarantun Kajuru saboda karuwar rashin tsaro.
Umarnin ya zo ne kwanaki kadan bayan an sace dalibai da malamai a makarantar firamare ta UBE da ke kauyen Rama, Birnin Gwari.
KU KARANTA KUMA: 2023: Ana halin fargaba yayinda PDP ke shirin yanke hukunci kan yankin da za ta baiwa tikitin Shugaban kasa
El-Rufai, yayin da yake magana bayan taron tsaro a ranar Talata, ya umarci dukkan makarantun jihar da su kasance a bude kuma ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na yin aiki tare da jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don magance matsalar rashin tsaro.
Amma kuma, a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 16 ga Maris 2021, Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta umarci duk Shugabannin makarantun Gwamnati da Masu zaman kansu da ke Kajuru su rufe makarantun ba tare da bata lokaci ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa karamar hukumar Kajuru na daya daga cikin kananan hukumomi biyar da ke fuskantar matsalolin tsaro a jihar.
Wasikar ta ce:
“Biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane da sauran nau’ikan matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu garuruwa da kauyukan karamar hukumar Kajuru, Babban Darakta-Janar na Hukumar Kula da Ingancin Makarantu na Kaduna ya umurce ni da in sanar da dukkan shugabannin makarantun gwamnati da masu zaman kansu a karamar hukumar Kajuru cewa a rufe dukkan makarantun nan take tun daga ranar 16 ga Maris 2021.
KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Nigeria ta ragargaji mayakan Boko Haram a wani arangama
“Kada makarantu su sake budewa har sai an umurce ku da yin hakan. Ku kasance masu kula da tsaro a kowane lokaci.”
A gefe guda, wasu tsagerun yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, wuta.
Daily Trust ta ruwaito cewa an kai wa motocin sarkin hari ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari da yammacin ranar Talata.
Za ku tuna cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya gana da Sarakunan gargajiyan jihar ranar Talata.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng