2023: Ana halin fargaba yayinda PDP ke shirin yanke hukunci kan yankin da za ta baiwa tikitin Shugaban kasa
- Kwamitin da Gwamna Bala Muhammed ke jagoranta na iya gabatar da rahotonsa a ranar Laraba, 16 ga watan Maris
- An daura wa kwamitin nauyin sake duba fitar da PDP tayi a babban zaben 2019
- An tattaro cewa tsarin yadda za a raba yankin da zai fitar da shugaban kasa a zaben 2023 na a cikin rahoton
Akwai fargaba a tsakanin mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayin da alamu suka nuna cewa nan ba da jimawa ba jam'iyyar za ta bayyana matsayarta kan batun raba tikitin takarar shugaban kasa a 2023.
Jaridar Sun ta rahoto cewa wannan na zuwa ne yayin da aka shirya kwamitin sake duba babban zaben jam’iyyar adawar ta 2019 don gabatar da rahotonta a ranar Laraba, 17 ga watan Maris.
Legit.ng ta tattaro cewa kwamitin, wanda aka kaddamar a shekarar 2020, karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.
An dora masa alhakin sake duba fitar da PDP tayi a zaben 2019 tare da bayar da shawarwarin da suka dace kan yadda za a inganta nasararta a cikin zaben gaba.
Jaridar ta ce rahoton kwamitin duba zaben PDP na 2019, wanda za a gabatar ga masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnoni, mambobin Kwamitin Aiki na Kasa (NWC) da sauransu za su tsara matakin raba mukamai don zaben 2023.
KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Nigeria ta ragargaji mayakan Boko Haram a wani arangama
Kawunan shugabannin PDP a fadin kasar ya rabu kan ko a bari yankin arewa ta ci gaba da rike tikitin takarar Shugaban kasa ko kuma a mika ta ga yankin Kudu.
Uche Secondus, shugaban PDP na kasa, ya bayyana a watan Disambar 2020, cewa jam'iyyar adawa na jiran kwamitin da Bala Mohammed ke jagoranta don ba ta damar yanke hukunci kan yankin da za a baiwa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.
Ya ce:
“Bayan babban zaben, mun kafa kwamiti don yin nazari da kimanta ayyukanmu tare da bayar da shawarwarin da suka dace.
KU KARANTA KUMA: Kasashen nahiyar Afrika 10 masu kudi mafi daraja a 2021
"Gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Bala Mohammed, shi ne yake jagorantar kwamitin kuma har yanzu yana kan aiki. Mun yi irin wannan lokacin da muka fadi zabe a shekarar 2015 lokacin da muka kafa kwamitin Sanata Ike Ekweremadu don duba abin da ya sa muka fadi."
A gefe guda, bangaren jam’iyyar PDP ta jihar Edo, ta ba uwar-jam’iyya shawara ta kai takarar shugaban kasa a zaben 2023 zuwa shiyyar Kudu maso kudu.
Jaridar Punch ta rahoto shugaban PDP na Edo, Mista Tony Aziegbemi, ya na cewa ya kamata mutumin Kudu maso kudu ya samu tikiti a 2023.
Tony Aziegbemi ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, 15 ga watan Maris, 2021, a lokacin da ya zanta da manema labarai a garin Benin, jihar Edo.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng