Da Ɗumi-Ɗumi: Danbarwa ta ɓarke a majalisar dattijai kan Kudirin samar da Hukumar kula da Jami'an tsaro

Da Ɗumi-Ɗumi: Danbarwa ta ɓarke a majalisar dattijai kan Kudirin samar da Hukumar kula da Jami'an tsaro

- Rikici ya ɓarke a zaman majalisar dattijai na yau kan wani kudiri da aka gabatar na ƙirƙirar hukumar kula da jami'an tsaro

- Rikicin ya ɓarke ne daga lokacin da shugaban marasa rinjaye na majalisar ya sake gabatar da kudirin domin yi masa karatu na biyu

- An fara karanta ƙudirin a zaman majalisar tun watan Maris din shekarar data gabata 2020

An yi kace nace a majalisar dattijai ranar Laraba bayan an samu rabuwar kai tsakanin yan majalisun kan kudirin dokar samar da hukumar kula da ayyukan jami'an tsaro.

KARANTA ANAN: 2023: Ana halin fargaba yayinda PDP ke shirin yanke hukunci kan yankin da za ta baiwa tikitin Shugaban kasa

Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe, shine ya kawo kudirin na kirkirar hukumar kula da jami'an tsaro, 2021 (SB.362).

Bayan ya kammala gabatar da bayanan sa, an samu karin bayanai daban daga sauran sanatocin majalisar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sanatoci takwas sun nuna goyon bayan su ga kudirin, yayin da guda shida suka yi watsi da shi.

Da Ɗumi-Ɗumi: Danbarwa ta ɓarke a majalisar dattijai kan Kudirin samar da Hukumar kula da Jami'an tsaro
Da Ɗumi-Ɗumi: Danbarwa ta ɓarke a majalisar dattijai kan Kudirin samar da Hukumar kula da Jami'an tsaro Credit: @NGRSenate
Asali: UGC

Rigima ta fara ne yayin da shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya buga sandar sa wanda hakan bai ma Abaribe dadi ba.

KARANTA ANAN: Ministocin Buhari 6 da za su iya ajiye mukamansu, su tafi takarar Gwamna a 2023

Abaribe ya mike inda ya nuna adawa da shugaban majalisar bisa doka ta 73 na dokokin majalisar.

A bisa wannan danbarwar data faru, dole ta sa majalisar ta sanar da shiga zaman kulle da misalin karfe 12:23 na rana.

A wani labarin kuma Hukumar NAFDAC ta bayyana cewa ba za'a dakatar da rigakafin COVID19 ba

Shugabar Hukumar NAFDAC ce ta fadi haka a wata fira da tayi da gidan talabishin na Channels TV

Tace ta yi imani cewa amfanin da rigakafin Astrazeneca ke da shi ya zarta illar ta saboda haka be kamata a dakatar da yin rigakafin ba.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262