Abdurrasheed Bawa ya bukaci ma'aikatan banki da su gaggauta bayyana kadarorinsu

Abdurrasheed Bawa ya bukaci ma'aikatan banki da su gaggauta bayyana kadarorinsu

- Hukumar EFCC ta bukaci dukkan ma'aikata banki a kasar Najeriya da su bayyana kadarorinsu

- Shugaban EFCC ne ya bayyana wannan bukata biyo bayan wata ganawa da shugaban kasa

- Yin hakan in ji shi yunkuri ne na ganin an dakile aikata laifukan sata ta yanar gizo da ake fama dashi

Hukumar EFCC a Najeriya ta umarci ma’aikatan banki da su bayyana kadarorinsu da suka mallaka ta kuma bada wa'adi zuwa ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2021, The Cable ta ruwaito.

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce sun tattauna kan kokarin da hukumar ke yi na kawar da laifukan kudi a kasar.

Bawa ya bayyana cewa an dauki matakin ne don duba rawar da bankuna ke takawa wajen rike kudaden da suka samu ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA: El-Rufai: Aikina shine tilasta doka ba yiwa 'yan bindiga wa'azin su tuba ba

Abdurrasheed Bawa ya bukaci ma'aikatan banki da su gaggauta bayyana kadarorinsu
Abdurrasheed Bawa ya bukaci ma'aikatan banki da su gaggauta bayyana kadarorinsu Hoto: The Cable
Asali: Twitter

"Bari kawai in bayyana wannan, mun fahimci cewa a karshen duk wani laifin kudi shine mai laifi ya samu damar samun kudaden da shi ko ita ta samu ba bisa ka'ida ba kuma muna cikin damuwa game da matsayin cibiyoyin kudi," in ji shi .

“Kuma mun tattauna, amma muna fatan duk cibiyoyin hada-hadar kudi, musamman ma ma'aikatan bankii, za su bayyana kadarorinsu kamar yadda doka ta tanada, kamar yadda Dokar Bayyana Kadarorin Ma’aikatan Banki ta tanada.

"Kuma cewa EFCC, idan 1 ga Yuni 2021 tazo, za ta bukaci wadannan takardun bayyana kadara, wadanda bankunan suka cika domin tabbatar da sharadin da muka gindaya na 1 ga Yuni hakika ma'aikatan banki sun bi shi."

Shugaban na EFCC ya koka kan yadda hukumar ta damke kimanin masu aikata laifuka ta yanar gizo kimanin 300 a fadin kasar tsakanin watan Fabrairu da Maris.

“A matsayina na matashi, ina kira ga dukkan matasa 'yan Nijeriya da su guji wadannan ayyukan ta’addanci na yanar gizo.

"Yana jawo munanan suna ga kasarmu, yana batawa kasarmu suna, haka kuma yana kokarin salwantar da jarin kasashen waje da muke bukata,” inji Bawa.

“Kuma ina kira ga dukkan iyaye, masu kulawa, da kuma ba shakka, dattawa a cikin al’umma, da su jawo hankalin wadannan matasa don su guji wadannan laifuka."

KU KARANTA: Ya fara zama abin dariya ma yanzu kam: Wike ya yi tsokaci game da sace ‘yan makaranta

A wani labarin, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya ce ya ba da shawarar nada Abdulrasheed Bawa ya zama shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da yiwa Tattalin Arziki zagon Kasa ne saboda tsananin kwazo da iya aiki.

Malami, a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust, ya ce sabanin rahotannin da ke cewa shi kadai ya zabi Bawa ya zama shugaban EFFC, an mika sunayen mutane hudu ga shugaban kasar don ya duba su sannan daga baya aka zabi Bawa.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel