Ya fara zama abin dariya ma yanzu kam: Wike ya yi tsokaci game da sace ‘yan makaranta

Ya fara zama abin dariya ma yanzu kam: Wike ya yi tsokaci game da sace ‘yan makaranta

- Gwamnan jihar Ribas ya yi tsokaci kan lamarin sace-sace a yankin Arewacin Najeriya

- Gwamnan ya bayyana cewa, lamarin sace dalibai na zama abin dariya a 'yan kwanakin nan

- Ya kuma zargi cewa, dole akwai lamarin sanya siyasa idan akayi duba da yawan sace-sacen

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana matsayin sace dalibai da sakinsu a yankin Arewacin Najeriya da 'yan bindiga ke yi da ‘abin dariya’. PM News ta ruwaito.

Wike ya yi magana ne a yayin ziyarar da karamin Ministan Noma, da Raya Karkara, Mustapha Baba Shehuri ya kai masa a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Fatakwal, ranar Litinin.

Gwamnan Ribas ya yi tambaya game da dalilin yawaitar satar yara a jere da kuma sake su ba da jimawa ba a yankin.

KU KARANTA: Da a sace yaranku, gwanda ku killace su a gida, Aisha Yesufu ga iyaye

‘Ya fara zama abin dariya ma yanzu kam’ Wike ya yi tsokaci game da sace ‘yan makaranta
‘Ya fara zama abin dariya ma yanzu kam’ Wike ya yi tsokaci game da sace ‘yan makaranta Hoto:@RiversHoopers
Asali: Twitter

“Na ga labarai, wani sata na 'yan bindiga a Kaduna tare da kwashe dalibai da malamai. Abin yana zama abin ban dariya. Jiya, kun dauki 300, kwana biyu bayan haka, kun sake su. Washegari, kun dauki wasu, awanni 24 masu bayan haka, an sake su.

“Don haka, mutane sun san inda suke. Kuna daukar mutane dari biyu da wani abu a cikin nisan kilomita 20 kuma babu wanda zai sani? Kuma a cikin awanni 24 masu zuwa an sake su. Menene gaskiyar lamarin da ke faruwa?

“Shin wani zai iya gaya mana gaskiyar abin da ke faruwa. Ya zama abin dariya. Kuma me yasa haka? Dalili shine saboda mun sanya siyasa a batun tsaro.”

KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda sun ceto wasu 'yan mata daga gidan sayar da jarirai

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta jaddada bukatar ‘yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan don kawo karshen hare-hare a makarantu da sace dalibai.

Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, wanda ya bayyana hakan a cikin wata hira da jaridar The Punch a ranar Litinin, ya nuna cewa gwamnati ba za ta iya tabbatar da tsaron kowace makaranta a kasar ba.

A cewarsa, gwamnati ta umarci makarantu su kai rahoton duk wata barazanar tsaro ga hukumar tsaro mafi kusa.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel