Dalilin da ya sa na bada shawarin nada Abdurrasheed Bawa shugaban EFCC, Malami

Dalilin da ya sa na bada shawarin nada Abdurrasheed Bawa shugaban EFCC, Malami

- Biyo bayan nada shugaban EFCC Bawa, wasu sun yi ta cece-kuce a kan sabon nadin nasa

- Ministan Shari'a Malami, ya bayyana dalilan da yasa ya bada shawarar a nada Bawa

- Daga cikin dalilansa, yace yayi duba zuwa ga iya aiki da kwarewa wanda Bawa ke da shi

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya ce ya ba da shawarar nada Abdulrasheed Bawa ya zama shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da yiwa Tattalin Arziki zagon Kasa ne saboda tsananin kwazo da iya aiki.

Malami, a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust, ya ce sabanin rahotannin da ke cewa shi kadai ya zabi Bawa ya zama shugaban EFFC, an mika sunayen mutane hudu ga shugaban kasar don ya duba su sannan daga baya aka zabi Bawa.

Malami ya kuma musanta alakarsa da shugaban na EFCC.

KU KARANTA: Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta

Dalilin da ya sa na bada shawarin nada Abdurrasheed Bawa shugaban EFCC, Malami
Dalilin da ya sa na bada shawarin nada Abdurrasheed Bawa shugaban EFCC, Malami Hoto: The Capital
Asali: UGC

“Na yi farin ciki cewa yawancin maganganun da ake ba sa sukar ikonsa, wayewar sa, kwarewar sa da kuma karfin hadewar sa. Ba a taba tuhumar ikon sa na isar da aikinsa a duk fadin kasar ba.

“Tambayar ita ce shin an yi adalci, ko an yi amfani da maslahar jama’a kasancewar an nada shugaban tare da la’akari da karfinsa da kuma iya aiwatar da aikinsa.

“Amsata ita ce eh. Yana da karfin iya aiki, iyawa da kuma tarihin hukumarsa na yin adalci ta hanyar kawo karin daraja ga hukumar,” in ji shi.

Malami ya ce kasancewar ya jagoranci bangarorin aiki uku na hukumar, takardun shaidar Bawa sun sanya shi a cikin sunayen da aka tura wa shugaban.

Malami ya lura da cewa Bawa "ya rike hukumomi da dama, wadanda suka hada da aiki a bangarori daban-daban a matsayin shugaban ayyuka, da suka hada da Fatakwal, Legas da Ibadan wadanda a ke ganin su ne manya-manyan wurare."

Ministan ya ce tun da ba a sauya dokar da ke kula da ayyukan EFCC ba, zargin da ake na nada Bawa zai murkushe wasu ayyukan hukumar da ba shi da tushe.

KU KARANTA: Baku isa ba: Shugaba Buhari ya gargadi 'yan bindigan da ke sace dalibai

A wani labarin daban, Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya bayyana a gaban wata babbar kotu da ke Ikeja don bayar da shaida a shari'ar zamba ta biliyan N1.4 da ta shafi wani kamfanin mai mai suna Nadabo Energy.

Bawa, kafin a tabbatar da shi a matsayin shugaban EFCC, ya bayyana a gaban kotun a bara a matsayin shaidan mai gabatar da kara, Vanguard News ta ruwaito.

Hukumar ta EFCC ta zargi Abubakar Ali Peters da kamfaninsa, Nadabo Energy da zargin yin amfani da takardun jabu don karbar N1,464,961,978.24 daga Gwamnatin Tarayya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.