El-Rufai: Aikina shine tilasta doka ba yiwa 'yan bindiga wa'azin su tuba ba
- Gwamnan jihar Kaduna ya sake jaddada cewa, ba zai yiwu ya tattauna da 'yan bindiga ba
- Ya ce ba aikinsa bane ya tsaya yana yiwa 'yan bindiga wa'azi ko rokon su aje makamansu
- A cewarsa, aikinsa shine tabbatarwa tare da tilasta bin doka da oda a matsayinsa na gwamna
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da 'yan bindiga da masu aikata laifi ba, The Nation ta ruwaito.
Ya ce aikinsa a matsayin Gwamna shi ne tilasta doka da gurfanar da masu laifi amma ba da'awar tuba da lallami a gare su ba.
El-Rufai ya maimaita matsayin gwamnatinsa yayin fadada taron majalisar tsaron jihar a zauren majalisar na gidan Sir Kashim Ibrahim a ranar Talata.
Baya ga mambobi na yau da kullum daga gwamnatin jihar, hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya, taron ya hada da shugabannin addinai da kuma bakin da aka gayyata daga kungiyoyin kwararru, ƙwadago da na fararen hula.
KU KARANTA: Ya fara zama abin dariya ma yanzu kam: Wike ya yi tsokaci game da sace ‘yan makaranta
“Ba za mu yi hulda da 'yan bindiga ko masu satar mutane ba. 'Yan kasa masu zaman kansu kamar malamai na iya yin hakan a cikin ikon su, don yi musu wa'azi da rokon su tuba. Muna kuma son su tuba amma ba aikinmu bane mu nemi su yi hakan,'' ya jaddada.
A cewarsa, hanya mafi kyau ta magance rikice-rikicen manoma da makiyaya, satar shanu da fashi da makami shi ne makiyaya su yi rayuwa ta zama waje daya don su zama masu amfani kuma su bai wa yaransu ilimi da kuma samun ingantaccen kiwon lafiya.
Gwamnan ya bayar da hujjar cewa, an daina kiwo irin na da ko kuma kiwon shanu a fili saboda bunkasar birane da karuwar jama'a domin yawancin hanyoyin da shanun ke bi sun zama garuruwa.
El-Rufai ya ce Gwamnatin jihar Kaduna na aiwatar da wani babban aiki na kiwo a Filin Kiwo dake Damau a karamar hukumar Kubau, ya kara da cewa aikin zai tallafawa makiyaya kusan 1,500.
Ya jaddada cewa aikin zai baiwa makiyaya damar kiwon shanunsu a wani wuri da ya kunshi wuraren kiwo, makaranta da Cibiyar Kiwon Lafiya ta matakin Farko tare da samar da abokan kasuwanci da ke shirye don siyan madarar shanu.
KU KARANTA: Da a sace yaranku, gwanda ku killace su a gida, Aisha Yesufu ga iyaye
A wani labarin daban, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana matsayin sace dalibai da sakinsu a yankin Arewacin Najeriya da 'yan bindiga ke yi da ‘abin dariya’. PM News ta ruwaito.
Wike ya yi magana ne a yayin ziyarar da karamin Ministan Noma, da Raya Karkara, Mustapha Baba Shehuri ya kai masa a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Fatakwal, ranar Litinin.
Gwamnan Ribas ya yi tambaya game da dalilin yawaitar satar yara a jere da kuma sake su ba da jimawa ba a yankin.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng