Rundunar 'yan sanda tayi ram da wasu 'yan ƙungiyar asiri a Abuja

Rundunar 'yan sanda tayi ram da wasu 'yan ƙungiyar asiri a Abuja

- Rundunar yan sanda ta cafke wasu mutane da ake zargin 'yan ƙungiyar asiri ne a babban birnin tarayya Abuja

- Mutanen da aka kama sun bayyana cewa, su 'yan wata ƙungiya ne da ta addabi yankin Gwagwa

- A zagayen da 'yan sandan sukayi ranar Jumu'a sun kuma cafke wasu da ake zargin yan fashi ne

Hukumar 'yan sandan birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane biyar da ake zargin aikata ayyukan asiri da kuma fashi a yankin Gwagwa da Lugbe, hanyar Airport.

Daga cikin wadanda ake zargin akwai; Peter Ajari mai shekaru 24, John mai shekaru 28 da kuma Emmanuel Agwu mai shekaru 26.

KARANTA ANAN: Yanzun nan: An yi bata-kashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga a filin jirgin sama na jihar Kaduna

'Yan sandan sun kama mutanen ne a wani aikin sinitiri da suka fita ranar Juma'a 12 ga watan Maris. Vanguard ta ruwaito.

Wadanda ake zargin sun bayyana cewa su mambobin ƙungiyar 'Aro Baga' ne wadanda suka addabi yankin Gwagwa dake birnin tarayya Abuja.

Abubuwan da aka samu a hannun su sun hada da karamar bindigar gargajiya guda daya da ragowar harsasai guda biyu.

Rundunar 'yan sanda tayi ram da wasu 'yan ƙungiyar asiri a Abuja
Rundunar 'yan sanda tayi ram da wasu 'yan ƙungiyar asiri a Abuja Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Ndume: Dalilan da zasu sa APC ba zata fito dan takara daga arewa ba

Haka zalika, jami'an ƴan sanda masu yaki da fashi a hukumar reshen Abuja, sun kama wata Blessing Nuhu mai shekaru 24 da Ifeoma Nnamuchi mai shekaru 31 da zargin fashi a yankin Lugbe.

Ifeoma Nnamuchi ita ce shugabar yan fashin mai mutane hudu dake aiki a rukunin Lugbe da Galadinmawa.

An dai kama sauran mutane biyun Charity Timothy mai shekaru 23 da Sunday Godwin mai shekaru 23 daga cikin wannan kunngiyar tun ranar 1 ga watan Maris, wanda kuma sun amsa cewa suna addabar wannan rukunin.

An samu mota ja guda daya kirar Volkswagen mai rajista BWR 903 HE da kuma wayar hannu guda daya a hannun waɗanda ake zargin.

"Dukkanin wadanda ake zargin za'a mika su gaban kuliya bayan kammala bincike" a cewar hukumar yan sandan ta bakin mai magana da yawun hukumar, ASP Yusuf Mariam.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sace wata yarinya 'yar shekara 18 a cikin gidan mahaifinta a jihar Kebbi

An sace Naja’atu daga gidan mahaifinta inda aka harbi wata mata Hajiya Nana Sanusi.

Yanzu haka tana karbar kulawar likita a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwanan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano. Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77

Source: Legit

Online view pixel