'Yan bindiga sun sace wata yarinya 'yar shekara 18 a cikin gidan mahaifinta a jihar Kebbi

'Yan bindiga sun sace wata yarinya 'yar shekara 18 a cikin gidan mahaifinta a jihar Kebbi

- An sace wata budurwa 'yar shekara 18 a gidan mahaifinta a wani yankin jihar Kebbi

- An kuma kashe wata mata a gidan har lahira a yayin da 'yan bindiga suka kai hari gidan

- Mayaimakin gwamnan jihar Kebbi ya jajantawa iyalai, tare da tabbatar da kare rayuwar al'umma

A safiyar jiya ne wasu ‘yan bindiga suka sace wata yarinya‘ yar shekara 18 mai suna Naja’atu Faruk, a garin Birnin Kebbi da ke jihar Kebbi, Leadership ta ruwaito.

An sace Naja’atu daga gidan mahaifinta inda aka harbi wata mata Hajiya Nana Sanusi. Yanzu haka tana karbar kulawar likita a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi.

KU KARANTA: An kashe matar tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Benue

'Yan bindiga sun sace wata yarinya 'yar shekara 18 a cikin gidan mahaifinta a jihar Kebbi
'Yan bindiga sun sace wata yarinya 'yar shekara 18 a cikin gidan mahaifinta a jihar Kebbi Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Mataimakin gwamnan jihar, Samaila Yombe Dabai wanda ya ziyarci gidan, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma ya ba da tabbacin jajircewar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Ya kara da cewa babu wani abinda zai hana a gurfanar da masu aikata muggan laifuka a jihar.

KU KARANTA: Jirgi mai saukar ungulu da sauran abubuwa 4 masu ban mamaki da Nigeria ta kera ta siyar a waje

A wani labarin, 'Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu mutum shida a yankin Erena da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Wannan shine hari na biyu da al'ummomin yankin ke gani cikin kasa da makonni biyu a jihar.

'Yan bindigar sun kai harin ne cikin tsakar dare dauke da muggan makamai. Wasu majiyoyi sun fadawa jaridar The Nation cewa ‘Yan bindigar sun fi 50 kuma sun kara da cewa wasu mutanen da dama sun samu rauni a kokarinsu na tserewa daga sace su.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel