Yanzun nan: An yi bata-kashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga a filin jirgin sama na jihar Kaduna

Yanzun nan: An yi bata-kashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga a filin jirgin sama na jihar Kaduna

- 'Yan bindiga sun sake kai hari filin jirgin saman jihar Kaduna domin kwamushe mutane

- Rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar 'yan bindigan tare da dakile harin

- An yi ba-ta-kashi tsakanin 'yan bidigan da sojoji kafin daga bisani aka fatattaki 'yan bindigan

Rundunar soji ta sake dakile wani yunkuri da wasu ‘yan bindiga dauke da makami suka yi na sace ma’aikatan jirgin sama da ke zaune a rukunin ma’aikata na hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) a filin jirgin saman Kaduna.

Wannan na zuwa ne kusan makonni biyun makamancin wannan yunƙurin tare da yin garkuwa da wasu ma'aikata 13 ciki har da ma'aikatan Hukumar NAMA da danginsa da na Hukumar NIMET lokacin da 'yan ta'addan suka kai hari a baya.

Yunkurin da aka yi na baya-bayan nan wanda ya afku a safiyar ranar Lahadi ya jawo artabu tsakanin 'yan bindigan da sojoji wadanda suka kutsa cikin filin jirgin don ceton wadanda abin ya shafa.

KU KARANTA: Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18

Yanzun nan: Sojoji sun sake dakile harin 'yan bindiga a karo na biyu a filin jirgin Kaduna
Yanzun nan: Sojoji sun sake dakile harin 'yan bindiga a karo na biyu a filin jirgin Kaduna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Leadership ta tattaro cewa 'yan bindigan, kamar yadda suke a da, na iya sake samun damar shigowa cikin rukunin gidajen ta hanyar titin jirgi na 23 da 05.

Lokacin da suka samu damar shiga unguwar, an bayar da rahoton cewa 'yan bindigan sun wuce kai tsaye zuwa ga inda mutane suke, suna haska fitilun wuta don gano hanyar da za su kai wa wadanda abin ya shafa.

Ma'aikatan da ke zaune da kananan yara da manya a halin yanzu an ce za su bar wuraren don neman wani wuri a wajen filin jirgin saman inda za su zauna lafiya.

Manajan Daraktan FAAN, Kyaftin Rabiu Yadudu, bayan harin na farko ya nace cewa ba za a rufe Filin jirgin Kaduna da aiki ba, saboda harin.

KU KARANTA: Ndume: Dalilan da zasu sa APC ba zata fito dan takara daga arewa ba

A wani labarin, Sojojin rundunar gaggawa ta 1 na rundunar Sojin Najeriya sun dakile wani yunkuri da wasu 'yan bindiga suka yi don sace daliban makarantar Sakandaren Kasa da Kasa ta Turkiyya da ke Rigachikun, Jihar Kaduna, in ji Sojojin, The Nation ta ruwaito.

Daraktan hulda da jama'a na rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima, a cikin wata sanarwa, ya yi bayanin: “Yin aiki da wata shawara kan abin da ke gabatowa na sace daliban makarantar, sojoji da sauri suka hada kai don kare makarantar daga‘ yan bindiga.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel