Ndume: Dalilan da zasu sa APC ba zata fito dan takara daga arewa ba

Ndume: Dalilan da zasu sa APC ba zata fito dan takara daga arewa ba

- Sanata Ali Ndume, ya bayyana dalilansa na cewa bai son dan takarar shugaban kasa daga arewa

- A cewarsa, hakan ba zai zama an yi adalci ba ace an sake tsayar da dan takara daga yankin arewa

- Ya kuma bayyana matsalar da mutan kudu ke da ita dake sanyawa 'yan arewa shakku kan rikon shugabancinsu

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce zai saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ace arewa ta samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na gaba, Daily Trust ta ruwaito.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijai, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da kungiyar Correspondents' Chapel, kungiyar 'yan jaridu ta Najeriya da Majalisar Tarayya ta shirya a ranar Asabar.

Ya ce duk wani yunkuri na ware yanki ga tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar zuwa arewa zai zama daidai da zango na uku bayan Shugaba Muhammad Buhari na kan wa’adi na biyu na mulki.

Sanata Ndume ya ce ta hanyar nuna adalci da daidaito, ya kamata wani yanki na kudancin kasar nan ya samar da dan takarar shugaban kasa na gaba a APC.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace wata yarinya 'yar shekara 18 a cikin gidan mahaifinta a jihar Kebbi

Ndume: Dalilan da zasu sa APC ba zata fito dan takara daga arewa ba
Ndume: Dalilan da zasu sa APC ba zata fito dan takara daga arewa ba Hoto: BBC
Asali: UGC

Ya ce: “Ina adawa da APC ta samar da dan takararta na shugaban kasa daga arewa. Yakamata dan takarar shugaban kasa na APC ya fito daga kudu.

“Na taba fada a baya kuma har yanzu zan sake cewa idan har muna da dan arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC, a wurina, ya yi daidai da zango na uku kuma ba tsarin mulki bane.

“Kundin tsarin mulkin APC ya ce shugaban kasa zai yi wa’adi biyu kuma mun ce to arewa ta yi wa’adi biyu.

“Idan ka ce arewa ta sake fito da dan takarar shugaban kasa, hakan na nufin za ku je karo na uku kenan, wanda hakan ba daidai ba ne kuma na yi imani da adalci da daidaito.

“Ya kamata a samu dan takara daga kudu - wannan na nufin, kudu maso kudu, kudu maso gabas da kudu maso yamma - ya karbi tikitin.

“Ga kudu maso gabas, bari nace a misali, kana so ka zama shugaban wannan gidan kuma kana kira a raba gidan, shin hakan zai yi aiki?

“Kuma ina ganin kudu maso gabas na bukatar yin tunani a kai. Wannan shine yake haifar da jita-jita ga 'yan arewa harma suke cewa suna son sake samun shugaban kasa.

"Idan kana son zama shugaban Najeriya, dole ne ka yi imani da hadin kan Najeriya. Ina goyon bayan dan takara ya zo daga ko'ina a kudu.”

KU KARANTA: Jirgi mai saukar ungulu da sauran abubuwa 4 masu ban mamaki da Nigeria ta kera ta siyar a waje

A wani labarin, Tsohon kakakin majalisar wakilai kuma dan takarar Gwamnan Ogun a jam'iyyar ADP na 2019, Dimeji Bankole ya koma jam’iyya mai ci ta APC.

Ya gana da shugaban jam'iyyar APC, Kwamitin Kula da na Shirye-shiryen Babban Taron (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni a Abuja tare da rakiyar Gwamnan Jigawa Abubakar Bagudu. Ganawar, wacce ta gudana a gidan shugaban jam’iyyar APC da ke Abuja, ta dauki kusan tsawon awa guda.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel