Bai kamata farashin litar man fetur ya zarce 70 Naira ba, inji PDP

Bai kamata farashin litar man fetur ya zarce 70 Naira ba, inji PDP

- Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta ce sam bai kamata farashin litar mai ta wuce 70 Naira ba a Najeriya

- Jam'iyyar na martani ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin ana saida litar mai 212 Naira a wasu sassan ƙasar nan

- PDP tayi kira ga gwamnatin APC da ta shawo kan lamarin don ceto ƙasar daga matsin da aka shiga

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta bayyana cewa bai kamata ƙasa kamar Najeriya ta siyarma da ƴan ƙasarta litar man petur ya haura 70 Naira ba saboda ƙarfin samar da petur ɗin da take dashi.

KARANTA ANAN: 'Yan bindiga sun sace wata yarinya 'yar shekara 18 a cikin gidan mahaifinta a jihar Kebbi

Jam'iyyar tayi nuni da cewa duk wani mataki na ƙoƙarin ƙara farashin man petur ɗin ka iya jawo babbar zanga-zanga da bazata haifar da ɗa mai ido ba.

PDP ta gargaɗi jam'iyyar APC me mulkin ƙasar nan a wani saƙo data fitar ta hannun sakataren yaɗa labaranta, Kola Ologbondiyan.

Sakon na zuwa ne bayan jita-jitar da akeyi cewa wasu gidajen man petur na siyar da lita ɗaya a kan 212 Naira a wasu sassan ƙasar nan. Channels TV ta ruwaito

Sannan kuma hukumomin gwamnati na jaddada cewa gwamnati bata da niyyar ƙara farashin litar mai a wannn watan na maris.

PDP ta bayyana cewa duk wani shiri na ƙara litar mai takai 212 naira ka iya tura yan najeriya sukai bango ta yadda ba zasu iya jurewa ba.

Bai kamata farashin litar man pefur ya zarce 70 Naira ba, inji PDP
Bai kamata farashin litar man pefur ya zarce 70 Naira ba, inji PDP Hoto: @NNPCgroup
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Wanne 'yan bindiga zasu dauka, jan kunne ko wa'adin da ka basu?, Dawisu ga Buhari

A bayanin sakataren labaran PDP yace:

"Jam'iyyar mu na ganin cewa, ƙokarin ƙara farashin man petur da akema gwamnatin APC a watan maris na nuna rashin damuwarta ga yan ƙasa kuma be dace ba."

"Gaskiya babu ta yadda 'yan najeriya zasu iya rayuwa da wannan ƙarin farashin, kuma hakan ka iya ƙara janyo taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar nan." a cewarsa.

Ya ƙara da cewa: "Yan najeriya sunkai maƙura wajen jure wahalar wannan gwamnatin ta APC da bata dace dasu ba, kuma jam'iyyar mu na damuwa sosai wajen abinda ka iya faruwa idan farshin litar man letur ɗin ta cigaba da hauhawa."

Kwanan baya, jam'iyyar hamayyar ta yi gargaɗin cewa, kasancewar yawan matasa da basu da aikin yi da ake dashi da kuma wasu matsalolin ka iya jawo babbar zanga-zanga idan aka ƙara farashin man petur ɗin.

Daga ƙarshe jam'iyyar tayi kira ga gwamnati da ta ceto ƙasar daga duk wata matsala da ka iya biyo baya idan aka kara farashin.

Ta kuma roki yan Najeriya da su kasance masu ɗa'a da bin doka sau da kafa.

A wani labarin kuma Shugabannin hafsun soji sun sake dira jihar Borno don fatattakar Boko Haram

Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya sun sake dira jihar Borno a karo na biyu don magance matsalar tsaro

Manufar ziyarar tasu ta biyu yana da nasaba da tantance halin da ake ciki na rashin tsaro a jihar

Asali: Legit.ng

Online view pixel