Shugabannin hafsun soji sun sake dira jihar Borno don fatattakar Boko Haram

Shugabannin hafsun soji sun sake dira jihar Borno don fatattakar Boko Haram

- Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya sun sake dira jihar Borno a karo na biyu don magance matsalar tsaro

- Manufar ziyarar tasu ta biyu yana da nasaba da tantance halin da ake ciki na rashin tsaro a jihar

- Shugabannin sun kuma ziyarci asibitin sojoji domin duba wadanda suka ji rauni a fagen daga

Yayin da sojoji ke tsananta yaki da masu tayar da kayar baya a Borno, babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor, da shugabannin hafsoshi, sun isa Maiduguri, a karo na biyu a cikin wata daya don tantance halin da ake ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake yiwa sojojin jawabi, a ranar Asabar, a hedkwatar "Operation Lafiya Dole" a Maiduguri, Irabor ya yaba musu saboda nasarorin da aka samu.

Ya kuma yaba musu kan jajircewa da juriya, ya kara da cewa akwai wani umarni da Shugaban kasa da Babban Kwamanda ya bayar wanda dole ne a cika su.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke dan sanda, sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Benue

Shugabannin hafsun soji sun sake dira jihar Borno don fatattakar Boko Haram
Shugabannin hafsun soji sun sake dira jihar Borno don fatattakar Boko Haram Hoto: Channels Television
Asali: UGC

“Abin da ya kamata in sanar da ku shi ne cewa muna da wani umarni daga gareshi (shugaban kasa) kuma dole ne a cimma wannan umarnin.

“Don haka, wannan shine dalilin da yasa muke aiki ba tare da bata lokaci ba. Duk batutuwan tashin hankali da rashin tsaro, musamman a tsakanin rundunar Operation Lafiya Dole, dole ne a kawo karshenta,” in ji Irabor.

Tun da farko, Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Farouq Yahaya, ya yaba wa CDS da shugabannin hafsoshin domin ziyarar, yana mai cewa hakan zai kara wa sojojin kwarin gwiwa matuka.

Yahaya ya ce "Muna da kwarin gwiwa kan wannan kokarin na CDS da shugabannin hafsoshin da suke tuntubarmu bayan kowanne sa'a."

Ya gode wa CDS da shugabannin rundunoni don amsawar da suka yi da sauri kan magance matsaloli, kuma ya ba su tabbacin sojojin na sadaukar da kai ga ayyukan da aka ba su.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa CDS da shugabannin hafsoshin sun kuma ziyarci Asibitin Sojoji na Runduna ta 7, don duba da sojoji da suka ji rauni dake jinya a asibitin.

KU KARANTA: Bayan yin allurar Korona, gwamnan Bauchi ya roki Buhari ya nemo kudin siyan kari

A wani labarin, Sojojin rundunar gaggawa ta 1 na rundunar Sojin Najeriya sun dakile wani yunkuri da wasu 'yan bindiga suka yi don sace daliban makarantar Sakandaren Kasa da Kasa ta Turkiyya da ke Rigachikun, Jihar Kaduna, in ji Sojojin, The Nation ta ruwaito.

Daraktan hulda da jama'a na rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima, a cikin wata sanarwa, ya yi bayanin: “Yin aiki da wata shawara kan abin da ke gabatowa na sace daliban makarantar, sojoji da sauri suka hada kai don kare makarantar daga‘ yan bindiga.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel