Wanne 'yan bindiga zasu dauka, jan kunne ko wa'adin da ka basu?, Dawisu ga Buhari

Wanne 'yan bindiga zasu dauka, jan kunne ko wa'adin da ka basu?, Dawisu ga Buhari

- Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin ganduje ya zargi Buhari da yin maganganu masu karo da juna

- Dawisu, wanda hukumar jami'an farin kaya ta kwamushe a watan da ya gabata, yace wa'adi ko jan kunne 'yan bindiga zasu dauka

- Ya yi wannan wallafar ne bayan Buhari ya ja kunne 'yan bindigan da ke sace 'yan makaranta akan tabarbara harkar ilimi

Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai ga gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ruda 'yan bindiga da 'yan ta'adda a kasar nan da wa'adin da yake basu tare da jan kunne.

Yakasai, wanda Ganduje ya sallama a watan da ya gabata saboda kalubalantar mulkin Buhari da jam'iyyarsa ta APC, ya sanar da hakan ne a ranar Asabar.

A ranar Juma'a ne jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kutsa kwalejin harkar noma da gandun dabbobi dake Kaduna suka kwashe dalibai.

KU KARANTA: Rikicin manoma da makiyaya: Ka gaggauta yin taron tsaron kasa, Tinubu ga Buhari

Wanne 'yan bindiga zasu dauka, jan kunne ko wa'adin da ka basu?, Dawisu ga Buhari
Wanne 'yan bindiga zasu dauka, jan kunne ko wa'adin da ka basu?, Dawisu ga Buhari. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

An gano cewa jami'an tsaro sun ceto dalibai 180 amma 39 na hannun masu garkuwa da mutanen.

A ranar Asabar, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce Buhari "ya bada jan kunne ga masu yunkurin zama 'yan ta'adda da kuma 'yan bindigan dake shiga makarantu. Ya ce kasar nan ba za ta bari a tabarbara mata harkar ilimi ba."

A yayin yin martani ga kakakin shugaban kasan,Yakasai ya wallafa, "A gaskiyar magana, kana ruda 'yan bindiga ko 'yan ta'adda. A makon da ya gabata a Zamfara ka basu wa'adin watanni biyu, a yau kuma jan kunne ka bada, wanne za su dauka da gaske Mallam Garba?

"Da a ce ni mahaifin daya daga cikin daliban makarantar kwana ne a cikin jihohin da lamarin ya shafa, zan cire da na ne kawai."

Yakasai da ne ga dattaijon Kano, Tanko Yakasai, wanda a watan da ya gabata aka tsare shi a ofishin hukumar jami'an tsaron farin kaya a kan zarginsa da caccakar Buhari kan lamarin tsaron kasar nan.

KU KARANTA: Da duminsa: Ragowar daliban makarantar da 'yan bindiga suka kai farmaki sun koma barikin sojoji

A wani labari na daban, a ranar Juma'a ne jihar Kaduna ta tashi da mummunan labarin sace dalibai mata a kwalejin harkar noma da gandun dabbobi da ke Mando a jihar Kaduna.

Makarantar na da nisan kasa da kilomita 15 daga makarantar horar da hafsoshin soji dake Kaduna (NDA).

A ranar Alhamis ne 'yan bindiga suka kai hari kananan hukumomin Igabi, Giwa da Chikun inda suka halaka mutane bakwai.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel