Kashiga Hankalinka Ko Mu Koya Maka Darasi, Gwmnan Rivers Ya Gargaɗii Ministan Buhari

Kashiga Hankalinka Ko Mu Koya Maka Darasi, Gwmnan Rivers Ya Gargaɗii Ministan Buhari

- Gwamnan Rivers, Nyesom Wike, ya gargaɗi ministan harkokin Niger-Delta da ya kiyayi yin magana akan jiharsa

- Gwamanan ya yi wannan magana ne bayan ministan ya ƙalubalanci gwamnonin kudancin ƙasar nan

- Senator Godswill Akpabio ya ƙalubalanci gwamnonin ne a kan kukan da suke na cewa gwamnatin tarayya bata kulawa da hukumar raya yankin yadda yakamata

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya gargaɗi ministan harkokin Niger-Delta, Senator Godswill Akpabio da ya daina magana akan jiharsa ta Rivers.

Gwamanan na magana ne bayan ministan ya maida martani ga ƙungiyar gwamnonin kudancin ƙasar nan a kan kukan da suke da cewa gwamnatin tarayya na yima hukumar raya Niger-Delta riƙon sakainar kashi.

KARANTA ANAN: Janar Buratai ya karyata rahoton cewa ya ci kudin makamai

Ƙungiyar gwamnonin kudu maso kuduncin ƙasar nan, ƙarƙashin jagorancin gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, bayan sun gudanarda wasu tarurruka A Patakwal babban birnin jihar rivers, ya ce basu jin dadin yadda ake cigaba da gudanar da Hukumar ta NDDC.

Ya kuma yi kira ga shuwagabanni dasu waiwayi hukumar dan susan halin da take ciki.

A jawabin, Ifeanyi Okowa, ya ce:

"Muna kira ga shugaban ƙasa, idan har bazai naɗa shugabannin hukumar yanzun ba, to kuɗaɗen biyan albashi kaɗai za'a turo sauran kuma a rike su har sai an naɗa masu kula da hukumar wanda sune zasu gudanar da kuɗaɗen kamar yadda doka ta tanadar."

Kashiga Hankalinka Ko Mu Koya Maka Darasi, Gwmnan Rivers Ya Gargaɗii Ministan Buhari
Kashiga Hankalinka Ko Mu Koya Maka Darasi, Gwmnan Rivers Ya Gargaɗii Ministan Buhari Hoto: @Govwike
Source: Twitter

Ya yin da ministan yaje Patakwal ranar talata ya bayyana cewa: "Gwamnonin basu da ikon baiwa shugaban ƙasa mejo janar Muhammadu Buhari Umarni akan ƙaddamar da wani abu na hukumar."

KARANTA ANAN: Rade-radin Rahama Sadau na neman miji: Jarumar tayi karin haske

Sannan ministan ya ƙalulabalanci gwamnonin da su bayyana abinda sukeyi da 13% na man petur da ake turo musu. Kamar yadda Punch ta ruwaito

Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da sabuwar sakateriyar ƙungiyar 'yan kasuwa (TUC), Gwamnan Rivers, Nyesom Wike, ya gargaɗi ministan da kada yayi kuskuren taɓashi.

A cewarsa: "Zamu tuna masa lokacin da yake gwaman (Akwa Ibom) yana mulkinsa ne kamar wani sarki. Akwai kuɗi sosai a wancan lokacin kuma ana canza dala ɗaya ta amurka zuwa Naira a kan N150 amma yanzun yakai N500. Akpabio nada kuɗi sosai a wancan lokacin."

"Akpabio bai cancanci yayi magana akan Rivers ba, bashi da wannn damar. Idan yanason magana to ya yi akan jihar sa ta Akwa Ibom, idan kuma yaƙi to zamu koya masa hankali anan," Inji gwamnan.

Wike ya ƙara da cewa: "Idan har Akpabio zai cigaba da magana akan mu, to zan koya mishi darasi, idan kuma ya cigaba da irin waɗannan maganganu to zansa ya yi dana sani, domin ni ba irin waɗannan gwamnonin bane da zai juya yadda yike so."

"Zan iya nuna bidiyo inda Buhari ke cemasa yaje ya koya daga gareni a kan abubuwan da mukeyi anan," A cewarsa.

Bayan haka gwamna Wike ya roƙi Ƙungiyoyin ƙwadigo na ƙasa da su farka su ceto ƙasar nan daga rashin iya shugabancin da take ciki, yana mai cewa ƙungiyar ta rasa bakin magana a ƙarkashin Mulkin Buhari.

A wani labarin kuma Gwamnoni PDP sun ce Zasu Goyi Bayan Gwamnatin Tarayya Kan Yaki Da Matsalar Tsaro

Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Tambuwal ne ya faɗi haka jim kaɗan bayan fitowarsu daga taro a Abuja

Gwamnonin sun ce ko kaɗan baza su saka siyasa a matsalar tsaron da ake fama dashi a ƙasar nan

Source: Legit.ng

Online view pixel