Janar Buratai ya karyata rahoton cewa ya ci kudin makamai

Janar Buratai ya karyata rahoton cewa ya ci kudin makamai

- Buratai ya aike sakon kar ta kwana kan zarginsa da badakalar kudin makamai

- Lauyansa ya bayyana cewa Monguno bai ambaci sunan Buratai a jawabinsa ba

- NSA Monguno ya fasa kwai kan kudin makamai da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro

Tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai, ya karyata rahoton cewa ya ci kudin da aka bada don sayan makamai lokacin da yake mulki.

Buratai wanda yayi murabus makonnin baya, ya bayyana hakan ta bakin lauyansa, Osuagwu Ugochukwu, ranar Juma'a.

Mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta'addan Boko Haram.

NSA Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma'a, 12 ga Maris.

Tsaffin hafososhin tsaron sune Janar Abayomi Olonisakin; Lt-Gen. Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; Air Marshal Sadique Abubakar, dukka masu murabus.

Tuni Monguno ya ce anyi masa mummunan fassara ne ba haka yake nufi ba.

Buratai ya bayyana cewa ko sau guda Monguno bai ambaci sunansa ba.

KU KARANTA: Mun nemi kudin makaman da muka baiwa su Buratai mun rasa, NSA Monguno yayi fallasa

Janar Buratai ya karyata rahoton cewa ya ci kudin makamai
Janar Buratai ya karyata rahoton cewa ya ci kudin makamai Credit: Presidency
Source: Twitter

KU KARANTA: Daga cikin yan majalisan dokokin tarayya 469, 19 kadai ne mata, ga jerinsu

Kun ji cewa Ofishin ONSA na mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro ya fito ya yi karin haske a a kan kalaman da ya yi a game da salwantar kudin makamai.

A wani jawabi da ONSA ya fitar, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya ce ‘yan jarida sun rikada kalamansa bayan hirar da ya yi da BBC Hausa.

Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan jawabi da Babagana Monguno ya yi, ya ce a hirar da aka yi da shi, babu inda ya nuna an yi awon-gaba da kudin makamai.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel