Rade-radin Rahama Sadau na neman miji: Jarumar tayi karin haske
- Jaruma Rahama Sadau ta musanta rahotannin dake yawo na cewa tana neman mijin aure da gaggawa
- A cewar jarumar kamar yadda ta wallafa, wannan zance ne na bogi kuma ba zata taba yin hakan ba
- A makon da ya gabata ne aka dinga yada cewa jarumar na neman miji, lamarin da ya fusata ta ba kadan ba
Fitacciyar jarumar fina-finai Rahama Sadau ta musanta zantukan dake yawo a kafafen sada zumuntar zamani inda ake cewa tana neman mijin aure.
A farkon makon nan ne aka fara yada cewa jarumar tana neman miji da gaggawa domin tana son yin aure.
A fusace jaruma Rahama Sadau ta je shafinta na Instagram inda ta musanta rahoton tare da yi wa masu caccakarta tatas.
KU KARANTA: Da duminsa: Ragowar daliban makarantar da 'yan bindiga suka kai farmaki sun koma barikin sojoji
Ta yi martani akan rahoton dake cewa: "Duk mai son aure na ya fito, na shirya yin aure yanzu”.
Ta sake wallafa sakon a shafinta na Facebook tare da rubutu mai musanta wallafar. Tace ba ita ta rubuta hakan ba.
"Bogi Bogi Bogi... Ban ce ba, kuma ban taba wallafa abu makamancin haka ba. Bogi ne kuma ba zan lamunci wannan ba."
A halin yanzu dai wannan wallafa ta sadau bata yi wa wasu daga cikin mabiyanta na kafafen sada zumuntar zamani dadi ba, wadanda dama tuni suka riketa kuma suke ganin laifinta na barin Kannywood ta koma Nollywood.
A yayin rubuta wannan rahoton, wallafarta ta Instagram ta samu sama da martani 10,000. Yayin da wasu suka aminta da wallafarta, wasu kuwa sun ga bata dace ba.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga wata makaranta a Kaduna, sun kwashe dalibai
A wani labari na daban, majalisar wakilan tarayyar kasar nan tace ta talauce kuma kasafin da aka fitar mata ba dole ya amfani 'yan Najeriya ba.
Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar ya sanar da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, cewa 'yan majalisar na cikin tsananin "fatara yayin da suke kokarin sauke nauyin mazabunsu dake kansu."
Kamar yadda The Cable ta ruwaito, 'yan majalisar tarayyar sun saba kokawa a kan albashin da ake biyansu na N800,000 da kuma N8.5 miliyan duk wata.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng