Shugaba Buhari ya tura dakarun soji 6,000 jihar Zamfara

Shugaba Buhari ya tura dakarun soji 6,000 jihar Zamfara

- Shugaba Buhari ya bada umarnin kara dakarun soji 6000 a jihar Zamfara domin karin tsaro

- Gwamnan jihar, Bello matawalle ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da manema labarai

- Ya sanar da yadda ya kwashe kwanaki hudu a Abuja yana tattaunawa da Buhari tare da masu ruwa da tsaki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin tura dakarun soji 6000 jihar Zamfara.

Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya sanar da hakan a wata sanarwa da yayi a yammacin Talata, Daily Trust ta wallafa.

Ya ce da kanshi ya dauki kwanaki hudu a Abuja yana bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran masu ruwa da tsaki a kan halin da tsaron jihar ke ciki.

"A cikin tattaunawar mu da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran manyan kwamandojin tsaro a Abuja, an yanke shawarar cewa za a tura karin dakaru 6000 jihar domin karawa jami'an tsaron dake jihar karfi.

KU KARANTA: Hotuna: Hafsoshin tsaro sun dira jihar Zamfara, sun shiga ganawa da Matawalle

Shugaba Buhari ya tura dakarun soji 6,000 jihar Zamfara
Shugaba Buhari ya tura dakarun soji 6,000 jihar Zamfara. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Nan babu dadewa zasu iso domin fara aiwatar da ayyukansu, kuma muna mika godiya ga gwamnatin tarayya. Idan za ku iya tunawa, shugaban kasa ya umarci jami'an tsaro da su harbe duk wanda suka kama da makami ba bisa ka'ida ba.

"Shugaban kasa ya amince da wani wa'adi wanda yace 'yan bindigan zasu iya miko makamansu domin zaman lafiya. Kamar yadda kuka sani mun samu nasarori a sasancinmu da 'yan bindiga.

"Gwamnatin jihar ta yanke hukuncin daukan wadannan matakan: sarakunan gargajiya da mafarauta su kasance a garuruwan su domin sanya ido a kan masu shiga da fita yankin.

"Yawon fiye da mutane biyu a babur ya haramta, babu yawon babura a kungiyance a dukkan fadin jihar," Matawalle yace.

Gwamna Matawalle ya kara da tabbatar da haramta ayyukan 'yan sa kai a jihar tare da cewa duk wanda aka kama da bindiga zai sha mamaki.

KU KARANTA: Matashiya mai 'ya'ya 2 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta

A wani labari na daban, jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona na AstraZeneca a ranar Talata. Tijjani Hussaini, shugaban kwamitin martani na jihar ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.

"Jihar Kano ta shirya karbar rigakafi. An sanar da NPHCDA cewa Kano za ta karba kasonta a yau. Mun yi tsammanin samunsa a jiya amma yau zamu samu aka ce," yace.

Ya ce jihar ta shirya kaso 70 na shirin fitar dashi tare da fara yi wa jama'a rigakafin bayan ta karba.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel