Jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona a ranar Talata

Jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona a ranar Talata

- A yau Talata ne jihar kano za ta karba nata kason na rigakafin cutar korona na AstraZeneca

- Tijjani Hussaini, shugaban kwamitin shirin ya tabbatar da cewa jihar ta shirya kashi 70 don karba

- Ya ce nan da mako daya jihar za ta kammala shirin da za ta fara yi wa 'yan jihar allurar rigakafin cutar

Jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona na AstraZeneca a ranar Talata. Tijjani Hussaini, shugaban kwamitin martani na jihar ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.

"Jihar Kano ta shirya karbar rigakafi. An sanar da NPHCDA cewa Kano za ta karba kasonta a yau. Mun yi tsammanin samunsa a jiya amma yau zamu samu aka ce," yace.

Ya ce jihar ta shirya kaso 70 na shirin fitar dashi tare da fara yi wa jama'a rigakafin bayan ta karba.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon gagarumin mai safarar miyagun kwayoyi, Bishi Taiwo, da NDLEA ta kama

Jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona a ranar Talata
Jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona a ranar Talata. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta shirya wurare 509 inda za ta adana rigakafin.

"Idan aka duba shirin da muke yi, za mu iya cewa mun yi shiri ya kai kashi 70 yanzu haka. Nan da mako daya, Kano za ta kimtsa fara yin rigakafin cutar korona a fadin jihar," yace.

A ranar Litinin, jihar Ogun ta zama jihar Najeriya ta farko da ta karba kasonta na rigakafin korona bayan cika sharuddan karba.

A ranar 2 ga watan Maris ne rigakafin cutar korona ya iso kasar nan, The Cable ta wallafa.

Hukumar NAFDAC ta amince da a yi amfani da rigakafin bayan tantancesa da tayi sa'o'i kadan kafin a kaddamar dashi.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin Kwara ta sake garkame makarantu 10 a kan rikicin Hijab

A wani labari na daban, tsohon karamin ministan wutar lantarki na Najeriya, Muhammad Wakil, zai zauna a gidan yari har zuwa ranar 31 ga watan Maris 2021 bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja.

Ana zargin Wakil da almundahanar kudade har N27 biliyan wanda aka ware domin biyan tsoffin ma'aikatan NEPA hakkinsu na murabus.

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ce ta gurfanar da Wakil a ranar Litinin a kan zarginsa da ake yi da laifuka biyu, Vanguard ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng