Matashiya mai 'ya'ya 2 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta

Matashiya mai 'ya'ya 2 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta

- Matashiyar mata mai shekaru 37 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta

- Lekan Agboola, magidanci ne mai mata daya da 'ya'ya biyu amma budurwarsa ta mutu a wurinsa

- Yace da kanshi ya kirata domin ta same shi a gida saboda ya dade basu hadu ba amma basu dade da fara shagali ba tace ga garinku

Wata mahaifiyar yara biyu mai suna Lugas ta rasa rayuwarta yayin da suke lalata da masoyinta, rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da hakan, The Nation ta ruwaito.

'Yan sanda sun sake tabbatar da cewa sun damke saurayin mai suna Lekan Agboola domin su binciko asalin silar mutuwar matar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, wanda ya zanta da manema labarai a garin Yola, ya ce an tsare Agboola a sashin binciken manyan laifuka na rundunar.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon gagarumin mai safarar miyagun kwayoyi, Bishi Taiwo, da NDLEA ta kama

Matashiya mai 'ya'ya 2 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta
Matashiya mai 'ya'ya 2 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Agboola yace Lugas ta kasance budurwarsa na tsawon shekaru uku kuma yana da mata daya da 'ya'ya biyu a Legas.

A yayin bayyana aukuwar lamarin, Agboola yace da kanshi ya kira marigayiya Lugas don ta same shi a gida.

Ya ce, "A ranar 24 ga watan Fabrairun 2021 wurin karfe 9 na safe. Na kira ta a waya inda na bukaci ta zo ta ganni domin na dade ban ganta ba. Tana zuwa muka fara shagalinmu amma babu dadewa ta fadi.

"A lokacin da na gane bata numfashi sai na kira wata kawata mace kuma na fada mata abinda ke faruwa. Ta shawarce ni da in mika ta asibiti inda aka tabbatar da ta mutu."

'Yan uwan marigayiyar sun zargi wata munakisa a labarin mutuwarta, hakan ne yasa suka bukaci rundunar 'yan sanda da ta gano silar mutuwar 'yar uwarsu.

KU KARANTA: Ngwuta, alkalin kotun kolin Najeriya ya rasu a garin Abuja

A wani labari na daban, ma'aikatar ilimi ta jihar Kwara ta soke hukuncinta na sake bude wasu makarantu 10 na jihar inda aka yi rikicin saka hijab.

Kamar yadda babbar sakatariyar ma'aikatar, Kemi Adeosun ta tabbatar, da farko an bukaci makarantun su bude a ranar Litinin amma an soke hakan.

Ta ce wannan hukuncin an yanke shi ne saboda wasu dalilan tsaro, Premium Times ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel