Gwamnatin Zamfara ta kuɓutar da wasu mutane 10 da akayi garkuwa dasu

Gwamnatin Zamfara ta kuɓutar da wasu mutane 10 da akayi garkuwa dasu

- Gwamnatin jihar zamfara ta sake samun nasarar kuɓutar da wasu mutane 10 da aka sace a Gwaram

- Daga cikin kuɓutattun akwai mahifin ɗaya daga cikin ɗalibai mata da aka sace a Jangeɓe

- Mutumin ya bayyana cewa sun haɗu da ɗiyar tasa acan amma ya nuna mata kar tasake ta nuna ta sanshi

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake samun nasarar kuɓutar da mutane 10 da akayi garkuwa dasu ba tare da ya biya ko sisi ba.

Mutanen da aka kuɓutar, sun ce masu garkuwa da mutanen sun sace su ne a yankin Gwaram dake karamar hukunar Talatan Mafara kuma sun ɗau tsawon wata biyu da sati biyu a hannunsu.

KARANTA ANAN: Ministan Buhari da matarsa sun sabunta rijistar jam'iyyar APC a Rivers

Daga cikin waɗan da aka kuɓutar akwai maza uku, harda mahaifin ɗaya daga cikin 'yan matan makarantar sakandiri ta Jangeɓe, da kuma wasu mata huɗu.

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Abubakar Dauran, ya bayyana cewa sun kuɓutar dasu ba tare da an biya kuɗin fansa ba, ta hanyar tattaunawar zaman lafiya.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar zata cigaba da tattaunawan sulhu domin samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar. Channels TV ta ruwaito

Kwamishinan ya kara da cewa:

"Mu shaida ne wajen cigaba da ake samu a ɓangaren tsaro, mun kuɓutar da mutane 10 da akayi garkuwa da su a Gwaram, Karamar hukumar Talatan mafara, wanda daga cikinsu akwai mahaifin ɗaya daga cikin ɗaliban Jangeɓe."

Gwamnatin Zamfara ta kuɓutar da wasu mutane 10 da akayi garkuwa dasu
Gwamnatin Zamfara ta kuɓutar da wasu mutane 10 da akayi garkuwa dasu Hoto: @Zamfara_state
Source: Twitter

"Nayi imani cewa inda ba tattaunawa muke yi ba, da bazamu samu nasarar kuɓutar dasu ba. Zamu cigaba da wannan sulhu kodan yanayin da muka tsinci kanmu a jihar Zamfara," a cewarsa.

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Burtaniya za ta mayar wa Nigeria naira biliyan 22 da Ibori ya sace

Kwamishinan ya ƙara da cewa, a kwanakin baya mun kuɓutar da ɗalibai mata su 279.

Kafin nan ma mun ƙwato muggan makamai a hannun ɗan Buharin Daji wanda ya miƙa wuya domin ya tuba yayi rayuwa kamar kowa.

Ɗaya daga cikin matan da aka kuɓutar tace sun kwashe sati biyu a dajin tare da 'yayansu.

Matar mai suna Raliyat tace:

"Mun kwashe sati biyu a dajin duk da ana matsanancin sanyi, bamu da wani abu da zamu rufe jikinmu.

"'Yan bindigan sun zo suna neman Ubanƙassn Gusau amma basu sameshi ba, sun sami mahifinshi suka kashe shi kuma suka tattara iyalanshi sukayi gaba dasu" a cewar Raliyat.

Matar ta ƙara da cewa:

"Sunce suna tausaya ma 'yayan mu amma basu sake mu ba. Suna bamu shinkafa da wake, mune muke girkawa kuma suna da tukwane a wajen, Allah ne kaɗai ya cece mu."

A wani labarin kuma Wani sanata ya caccaki gwamnatin Buhari da sakewa 'yan bindiga fuska

A cewarsa, gwamnatin Buhari ta dauki 'yan bindiga da 'yan ta'adda kamar yara, an barsu suna abinda suke so

Ya bukaci gwamnati da ta bada umarnin murkushe 'yan ta'adda bawai umarnin harbe masu rike AK-17 ba.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit.ng

Online view pixel