Ministan Buhari da matarsa sun sabunta rijistar jam'iyyar APC a Rivers
- Ministan sufuri Rotimi Amaechi tare da Matarsa Dame Amaechi sun sabunta zama cikakkun 'yan jam'iyyar APC
- Ma'auratan sunje runfar zaɓen su mai lamba 14 dake karkashin karamar hukumar Iwerre Don sabunta katin su na zama yan APC
- Amaechi ya yabawa wakilan jam'iyya da ke kula da aikin din rijistar
Ministan sufuri Chibuike Amaechi Tare da me ɗakinsa Dame Judith Amaechi sun sabunta rijistar su da jam'iyyar APC a jihar Rivers.
Ma'auratan sun sabunta rijistar su ne a runfa ta 14, dake ƙarƙashin unguwa ta takwas a garin Ubima, dake karamar hukumar Ikwerre, jihar rivers.
KARANTA ANAN: Arewa ga naku: Ƴar Kano ta ƙera manhajar shigar da ƙorafin fyaɗe
Kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito, Ministan da matarsa sun sabunta rijistar ne ranar Litinin.
Shugaban kwamitin yin rijista da kuma sabunta rijistar jam'iyyar ta APC, Mr Kola Omotinugbon, ya yabawa uwar jam'iyyar bisa nuna halin dattako da takeyi wajen gudanar da aikinsu.
A lokacin da yake bawa Ministan sufuri katinsa, shugaban kwamitin yace da shi da matarsa an sabunta musu rijista a matsayin 001 da kuma 002 a runfar zaɓen.
"Bayan cike bayanansa da ministan yayi, an tabbatar masa da sabunta zaman shi cikakken ɗan jam'iyya," a cewar shugaban kwamitin.
KARANTA ANAN: Attajirin Yariman Saudiyya zai siya ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Faransa
Shugaban kwamitin riƙo na jam'iyyar APC a karamar hukumar Ikwerre, Eze Frank Aribodor, ya bayyana aikin sabuntawar a matsayin wanda akayi cikin kwanciyar hankali ba tare da an sami matsala ba.
Shugaban APC ya ƙara da cewa: "Kuna ganin yadda ministan sufuri ya ɗaga katinsa na zama cikakken ɗan jam'iyyar APC, don haka masu bukatar yin rijista suzo, waɗanda ma sukayi a baya suzo a sabunta musu."
Daga ƙarshe minista Amaechi ya godewa wakilan jam'iyyar APC dake kula da sabunta zama ɗan jam'iyya ko kuma rijistar zama ɗan jam'iyyar APC.
A wani labarin kuma An ci gaba da sauraran kara kan batun sanya dala a aljihu da aka gano Ganduje nayi
Lauyoyin Jaafar Jaafar sun koka kan ganin sabbin lauyoyi da Ganduje ya turo gaban kotun
Alkalin kotun, ya dage karar bayan watsi da kokensu zuwa wani lokaci don ci gaba da zama.
Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.
Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd
Asali: Legit.ng