Wani sanata ya caccaki gwamnatin Buhari da sakewa 'yan bindiga fuska

Wani sanata ya caccaki gwamnatin Buhari da sakewa 'yan bindiga fuska

- Wani sanata dan jam'iyyar PDP ya kalubalanci gwamnatin Buhari da sake wajen yakar 'yan ta'adda

- A cewarsa, gwamnatin Buhari ta dauki 'yan bindiga da 'yan ta'adda kamar yara, an barsu suna abinda suke so

- Ya bukaci gwamnati da ta bada umarnin murkushe 'yan ta'adda bawai umarnin harbe masu rike AK-17 ba

Tsohon sakataren yada labarai da shirye-shirye na jam'iyyar PDP, Anietie Okon, ya nuna bacin ransa ga gwamnatin tarayya kan yadda take mu'amala da 'yan ta'adda da 'yan bindiga a kasar, yana mai bayyana martanin gwamnati kan 'yan ta'adda a matsayin mara gamsarwa.

Okon, wani tsohon dan majalisar dattijai daga jihar Akwa ibom, ya yi mamakin dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta dirka a kan masu tayar da kayar baya a yankin Kudu Maso Gabas da cikakken karfin soja, a maimakon sanya karfin ta kan ‘yan bindiga, The Gurdian ta ruwaito.

“Abin takaici ne yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke mu'amala da masu tayar da kayar baya da 'yan bindiga kamar yara, ta bar su suna gudanar da ta'addanci yadda suke so a wasu sassan arewacin kasar na azabtarwa da wulakanta 'yan Najeriya.

KU KARANTA: Gwamna matawalle ya tsige sarkin Maru da wani saboda zargin tallafawa ta'addanci

Wani sanata ya caccaki gwamnatin Buhari da sakewa 'yan bindiga fuska
Wani sanata ya caccaki gwamnatin Buhari da sakewa 'yan bindiga fuska Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

“Halin da ake ciki yana bai wa 'yan Najeriya matukar damuwa cewa babban aikin gwamnati, wanda shi ne tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ba shi da tabbas a karkashin gwamnatin Buhari."

Ya yi ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya ta ayyana yaki a kan yankin Ibo ta hanyar tura jiragen sama na soji wadanda ya kamata a yi amfani da su wajen murkushe 'yan ta'adda, 'yan bindiga, masu sace mata da kananan yara a Zamfara, Kaduna da sauran sassan kasar.

Okon ya bayyana umarnin da shugaban kasa ya bayar na kwanan nan na harbe wadanda ke dauke da bindigar AK47 a matsayin wanda bai dace ba, yana mai cewa jami'an tsaro na bukatar izini don murkushe masu tayar da kayar baya da 'yan bindiga ne maimakon wannan umarnin.

KU KARANTA: Sufeto-Janar na 'yan sanda Adamu: Zan iya zama daram a ofis har zuwa 2023 ko 2024

A wani labarin, Jami'an tsaro a Kaduna sun tabbatar da kashe akalla 'yan bindiga hudu a wani kwanton bauna da aka yi a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

An kwato bindigogi uku da gatari daya daga hannun 'yan bindigar, wadanda suka kasance 'yan kungiyar ta'addancin da ke addabar sassan jihar. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da kisan 'yan bindigan.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel