Yanzu-yanzu: Burtaniya za ta mayar wa Nigeria naira biliyan 22 da Ibori ya sace

Yanzu-yanzu: Burtaniya za ta mayar wa Nigeria naira biliyan 22 da Ibori ya sace

- Kasar Burtaniya (UK) za ta mayarwa Nigeria zuzurutun kudi £4.2m da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya sace

- Burtaniya ta bakin jakadarta a Nigeria, Catriona Laing ta ce an gano kudaden ne daga hannun abokai da yan uwan tsohon gwamnan

- Laing ta ce kasar Burtaniya ba za ta cigaba da zama kasar da masu karkatar da kudaden satar za su rika ajiya ba

Burtaniya ta ratabba hannu kan yarjejeniyar fahimta inda za ta dawo wa Nigeria da zunzurutun kudi fam miliyan 4.2 (N22,615,572,000) na kudade da kadarori da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya sace.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da jakadar Burtaniya a Nigeria, Catriona Laing ta fitar a Abuja, babban birnin jihar, rahoton The Punch.

Yanzu-yanzu: Burtaniya za ta dawo wa Nigeria naira biliyan 22 da Ibori ya sace
Yanzu-yanzu: Burtaniya za ta dawo wa Nigeria naira biliyan 22 da Ibori ya sace. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A cewar Channels TV, Laing ta sanar da hakan ne a wurin ratabba hannu kan yarjejeniyar da dakin taro na ma'aikatar shari'a.

DUBA WANNAN: Alƙali ya bada umurnin rataye mutumin da ya kashe mahaifinsa ya birne shi a masai

Ta ce an kwato kudaden ne daga hannun abokai da iyalan tsohon gwamna.

Ta nuna rashin jin dadinta kan yadda yan Nigeria da dama ke karkatar da kudade zuwa Burtaniya wadda hakan na shafar amintaka da ke tsakanin kasashen biyu.

Laing ta ce Burtaniya ba za ta cigaba da zama wurin da barayin gwamnati za su rika kai kudin satarsu ba.

Atoni Janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami ya ce dawo da kudaden da aka sace na daga cikin kokarin da gwamnati mai ci yanzu ke yi na yaki da rashawa.

KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

Ya ce za a yi amfani da kudin wurin aikin ginin gadar Niger ta biyu, titin Abuja zuwa Kano da Lagos zuwa Ibadan.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel