Rigakafin Korona: Ƙungiyar matan gwamnoni sun yi kira ga gwamnati 'kada su mance da su'

Rigakafin Korona: Ƙungiyar matan gwamnoni sun yi kira ga gwamnati 'kada su mance da su'

- Matan gwamnoni sun yi kira ga gwamnatin tarayya da kada ta mance da su wajen yin rigakafin corona

- A cewar matan suma suna da rawar da zasu taka a kowanne fannin shugabanci

- Matan sunyi kira da a ƙara bawa mata dama a fannin shugabancin ƙasar nan, domin suma akwai matsalolin da zasu iya warwarewa

Ƙungiyar matan gwamnonin ƙasar nan sun yi kira ga gwamnatin tarayya a kan kada su mance da mata wajen rarraba rigakafin cutar corona.

Kungiyar ta yi wannan kira ne a wani saƙo da ta fidda dan tunawa da ranar mata ta duniya ran litinin.

KARANTA ANAN: Zaɓen 2023: Jam'iyar PDP ta bugi ƙirjin zata dawo da martabar Najeriya bayan ta ƙwace mulki

Saƙon ya ƙunshi sa hannun Shugabar kungiyar, Erelu Bisi Fayemi, da shugabar kungiyar matan gwamnonin arewa, Dr Amina Abubakar Bello, da kuma shugabar matan gwamnonin kudu, Mrs Betsy Obaseki.

Matan gwamnonin sun ce yakamata ace suma anyi musu rigakafin don su nuna wa mutane ingancinta.

"Duk da muna farfaɗowa daga wannan cutar da muka tsinci kanmu a ciki, muna kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da daidaito wajen samun rigakafin." a cewar matan.

Rigakafin corona: Ƙungiyar matan gwamnoni sun yi kira ga gwamnati 'Kada ku mance da mu'
Rigakafin corona: Ƙungiyar matan gwamnoni sun yi kira ga gwamnati 'Kada ku mance da mu' Hoto: @aishambuhari
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona

Sun ƙara da cewa: "Muna kira ga mata da su amince a musu allurar rigakafin da zaran damar hakan ta samu, mu kan mu za'ayi mana don mu tabbatar muku cewa rigakafin mai inganci ce."

Ƙungiyar matan sun kara yin kira da abar mata su fito a dama dasu a fannin shugabanci, domin akwai matsaloli dayawa da mata zasu iya warwarewa.

"Muna da kwarin gwuiwar cewa, idan aka ƙarfafa mata suka zama shuwagabanni, to za'a sami hanyoyi da dama wajen warware matsalolin da muke fuskanta," a cewar matan gwamnonin.

A matsayin mu na matan gwamnoni zamu cigaba da bawa mazajen mu goyon baya Kuma zamu tuna musu haƙƙin dake kansu na samar da tsaro, kare rayukan al'umma da kuma samar da ayyukan yi musamman ga mata.

A wani labarin kuma Jam'iyar APC tayi Allah wadai da kashe-kashen da akeyi a jihar Ekiti

A sanarwar da jami'in yaɗa labarai na jam'iyar ya fitar ya yi Allah wadai da kisan wasu manoma biyu da akayi kwanan nan a yankin Isaba

Bayan haka jam'iyar (APC) tayi kira ga jami'an tsaro da su ƙara ƙaimi don ganin sun kaɗe rayukan al'umma.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit

Online view pixel