Jam'iyar APC tayi Allah wadai da kashe-kashen da akeyi a jihar Ekiti

Jam'iyar APC tayi Allah wadai da kashe-kashen da akeyi a jihar Ekiti

- Jam'iyar (APC) mai mulki reshen jihar Ekiti tayi Allah wadai da kashe-kashen da akeyi a yankunan jihar musamman wanda akayi kwanan nan a yankin Isaba.

- A sanarwar da jami'in yaɗa labarai na jam'iyar ya fitar ya yi Allah wadai da kisan wasu manoma biyu da akayi kwanan nan a yankin Isaba

- (APC) tayi kira ga jami'an tsaro a jihar da su ƙara ƙaimi don ganin an daƙile faruwar lamarin nan gaba

Jam'iyar (APC) reshen jihar Ekiti ta nuna damuwarta matuƙa akan kashe-kashen da ake yawan samu a wasu yankunan jihar. Jaridar Vanguard ta wallafa.

Ta bakin jam'in yaɗa labarai na riƙon kwaryar jam'iyar, Ade Ajayi, ya yi Allah wadai da kisan da akayi wa wasu manoma a yankin Isaba na jihar.

KARANTA ANAN: Gwamnan Ekiti ya kai ziyara ga iyalan manoman da makiyaya suka kashe

(APC) ta bayyana rashin jin dadinta duk da cewa gwamnan jihar, Kayode Fayemi, nayin iya bakin kokarinsa na ganin an wanzar da zaman lafiya a faɗin jihar.

"Babu kokwanto gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Kayode Fayemi tana yin duk abu mai yuwu wa don ganin ta kare rayukar talakawanta mazauna jihar," a cewar Ajayi.

Jam'iyar APC tayi Allah wadai da kashe-kashen da akeyi a jihar Ekiti
Jam'iyar APC tayi Allah wadai da kashe-kashen da akeyi a jihar Ekiti Hoto @APCUKingdom
Source: Twitter

Ajayi ya kara da cewa: "Muna Allah wadai da waɗannan kashe-kashen da wasu tsiraru keyi a yankunan jihar."

KARANTA ANAN: IWD: Fadar shugaban ƙasa ta lissafa mata 50 da ke riƙe da madafan iko a gwamnatin Buhari

"Abun takaici ne wasu tsirarun mutane na ɗaukar doka a hannunsu ta hanyar aikata miyagun ayyuka dake barzana ga zaman lafiya a jihar," Ajayi ya faɗa.

(APC) na fatan duk shirye-shiryen da gwamnatin jihar keyi, da kuma binciken da sukeyi ya samu nasara akamo waɗan da ke aikata wannan ta'addancin.

Bayan haka jam'iyar (APC) tayi kira ga jami'an tsaro da su ƙara ƙaimi don ganin sun kaɗe rayukan al'umma.

"Jami'an tsaro su tabbatar da sun kamo waɗanda keda hannu a faruwar lamarin kuma amika su ga shari'a don fuskantar hukunci daidai da abinda suka aikata," inji (APC).

Daga ƙarshe, jam'iyar tayi fatan dawowar zaman lafiya a faɗin jihar, domin a cewarta hakane kaɗai zai ba gwamnatin jihar damar yin aikinta yadda ya kamata.

A wani labarin kuma An yankewa wasu 'yan Nigeria biyu hukuncin kisa a Ghana

Wata babbar kotu dake garin Sekondi na ƙasar Ghana ta yanke wa wasu 'yan Najeriya biyu hukuncin kisa.

Hukuncin ya biyo bayan tabbatar da laifin su na sace wasu mata huɗu da kuma kashe su.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit.ng

Online view pixel