Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona

Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona

- A ci gaba da yin allurar rigakafin Korona, Garba Shehu da sauran na kusa da Buhari sun yi allurar

- Hakazalika Garba Shehu ya bayyana rashin zafin allurar da kuma cancantar dukkan 'yan Najeriya su yi

- Ya kuma bayyana dalilinsa na yin allurar da cewa shi dan Najeriya ne mai kishin kasar

A ci gaba da aikin allurar riga-kafin Korona, Shugaban Ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Yada Labarai, Garba Shehu sun yi kashi na farko na allurar Korona na AstraZeneca.

Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona
Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Har ila yau, Sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Tijjani Umar da Shugaba kuma Babban Jami'in Hukumar Yaki da Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya), Channels Tv ta ruwaito.

Babban jami’in jinya, Dr Esther Ibrahim ne ya basu rigakafin a Cibiyar Kulawa ta Musamman na Asibitin Gwamnati dake Abuja.

KU KARANTA: Korarren hadimin Ganduje, Yakasai a karshe dai yayi magana

Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona
Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Shugaban Ma’aikatan bayan yin allurar ya bayyana rigakafin a matsayin mara ciwo.

Ya ce kawai yana bin sawun Shugaban ne a matsayinsa na dan Najeriya mai kima. Ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya da suka cancanta da su gabatar da kansu don yin rigakafin domin Najeriya ta samu kariya daga Korona.

Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona
Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Shima da yake jawabi a takaitaccen taron, Babban Sakatare na Fadar Gwamnatin, Tijjani Umar ya ce akwai bukatar gwamnati ta kare ‘yan kasarta ta hanyar samar da rigakafin COVID-19.

KU KARANTA: Jihar Katsina ta gurfanar da Dr Mahadi Shehu a gaban kotu da zargin batanci

A wani labarin, Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai sha wata wahala ba bayan yin allurar AstraZeneca ta Korona, TheCable ta ruwaito.

Buhari da Osinbajo sun yi allurar rigakafin a fadar shugaban kasa dake Abuja, ranar Asabar.

A wani yunkuri na kawar da fargabar ‘yan Najeriya, Shehu ya tabbatarwa 'yan kasar amincin allurar rigakafin, yana mai cewa shugaban “ya ji garau ya ci gaba da harkokinsa” bayan an yi masa rigakafin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel