Zaɓen 2023: Jam'iyar PDP ta bugi ƙirjin zata dawo da martabar Najeriya bayan ta ƙwace mulki

Zaɓen 2023: Jam'iyar PDP ta bugi ƙirjin zata dawo da martabar Najeriya bayan ta ƙwace mulki

-Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ta lashi takobin zata dawo da martabar Najeriya bayan ta ƙwace mulki a shekarar 2023

- PDP tayi ikirarin cewa sun samu jituwa a tsakanin 'yayanta kuma ta shirya tsaf domin ƙwace mulki daga jam'iya mai mulki a zaɓen dake tafe

- Ta kuma lashi takobin gyara najeriya don dawo da al'amura yadda suke kama daga haɗin kan ƙasa, da kuma dawo da martabar ƙasa

Babbar jam'iyyar adawa ta kasar nan (PDP) tasha alwashin dawo da martabar Najeriya da zarar ta kwace mulki a shekarar 2023, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

KARANTA ANAN: An yanka ta tashi: ‘Yan Sanda sun cafke ‘Yan OPC da su ka kama 'Shugaban 'Yan bindiga'

Jam'iyyar ta kuma lashi takobin kwace mulkin daga jam'iyya mai mulki ta (APC) a zabe mai zuwa kuma zata dawo da martabar ƙasar nan.

A wani saƙo da jam'iyar ta fitar jiya ta hannun sakataren labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya ce jam'iyarsa a shirye take ta fusakanci ko wane ƙalubale.

Zaɓen 2023: Jam'iyar PDP ta bugi ƙirjin zata dawo da martabar Najeriya bayan ta ƙwace mulki
Zaɓen 2023: Jam'iyar PDP ta bugi ƙirjin zata dawo da martabar Najeriya bayan ta ƙwace mulki Hoto: @pdpvanguard
Source: Twitter

"Zamu dawo da al'amura daidai da kyakkyawan shugabanci, sannan zamu dawoma da ƙasar mu zaman ƙafiya, da haɗin kai, da kuma farfaɗo da tattalin arziƙinta." a cewar Kola.

KARANTA ANAN: Kashin wasu samari ya bushe, ‘Yan Sanda sun damke su a wajen bikin ‘Yan luwadi

Ya ƙara da cewa tsarin jam'iyyarsu na yanki-yanki yasha banban dana jam'iyya mai milki (APC), kuma hakan na nuni da cewa sun shirya tsaf don ƙwace mulki a zaɓe mai zuwa.

"A yanzun munsami fahimtar juna mun zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, wanda hakan ke nuni da tsarin demokaraɗiyya a cikin gida, kuma zamu maida jin daɗin al'umma saman namu," a cewar jam'iyar.

A wani labarin kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya aikewa da mataimakinsa kalaman jinjina yayinda yake bikin ƙara shekara.

Mai girma shugaban kasa ya fitar da jawabi ne a jiya ta bakin mai magana da yawun bakinsa, Malam Garba Shehu, ya na yabon Farfesa Yemi Osinbajo.

Buhari ya ce Osinbajo mutum ne mai kishi, saukin hali, hakuri da sanin-aiki.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit.ng

Online view pixel