Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya kamata duk yan Najeriya su yi rigakafin korona

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya kamata duk yan Najeriya su yi rigakafin korona

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bayani na farko a hukumance bayan karbar allurar rigakafin COVID-19

- Shugaban na Najeriya ya bayyana dalilin da ya sa akwai bukatar ‘yan kasa su karbi rigakafin

- Gwamnatin tarayya na fatan yi wa yan Najeriya sama da kashi 70% allurar rigakafi a shekarar 2021 da 2022

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya da suka cancanta da su karbi allurar rigakafin COVID-19 domin kare kansu daga kamuwa da cutar.

Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar Asabar, 6 ga Maris, jim kadan bayan ya karbi kashi na farko na rigakafin korona na AstraZeneca, hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana a cikin wata sanarwa.

KU KARANTA KUMA: Ka daina nema wa 'yan fashi afuwa, gwamnan Katsina ya wanke Sheikh Gumi

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya kamata duk yan Najeriya su yi rigakafin korona
Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya kamata duk yan Najeriya su yi rigakafin korona Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ya ce:

‘’Na karbi rigakafina na farko kuma ina so na yaba wa duk ‘yan Najeriya da suka cancanta, su yi hakan domin a kare mu daga cutar.

"Alurar rigakafin zai kare kasar daga cutar Coronavirus. Hakazalika ina kira ga duk 'yan Najeriya da suka cancanta da su gabatar da kansu kuma a yi musu rigakafin bisa ga tsarin fifikon da aka riga aka tsara, a wasu cibiyoyin da aka ware kawai.”

Buhari ya roki dukkan gwamnatocin jihohi, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da su tattara mutane a kananan hukumominsu don yin rigakafin.

Ya yaba wa kamfanoni masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki wadanda suka goyi bayan martanin Najeriya game da cutar.

A baya mun ji cewa a ranar Asabar ne aka yiwa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari allurar rigakafin COVID-19, The Punch ta ruwaito.

Buhari ya yi rigakafin ne da misalin karfe 11.51 na safe a wani takaitaccen bikin da manyan jami’an gwamnati suka halarta a dakin taro na New Banquet da ke Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

KU KARANTA KUMA: Zamfara na jiran ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan sojan da ke kai wa yan bindiga kayayyaki

Babban likitan kansa, Dr Shuaib Rafindadi Sanusi ne ya yiwa shugaban kasar allurar ta rigakafin, yayin da mataimakin shugaban kuma Dr Nicholas Odifre, likita na musamman ga mataimakin shugaban kasar, in ji jaridar The Nation.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel