Ka daina nema wa 'yan fashi afuwa, gwamnan Katsina ya wanke Sheikh Gumi
- A 'yan baya-bayan nan, Sheikh Gumi yana ta kira ga gwamnatin tarayya da ta yi afuwa ga' yan ta'addan da ke yin barna a kasar
- Gwamna Masari na Katsina baya goyon bayan wannan kuma ya soki malamin addinin musulincin akan bada shawarar hakan
- Gwamnan na da ra'ayin cewa mai laifi, mai laifi ne kuma babu wata hujja da za ta wanke abin da suke yi wa 'yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya nuna damuwarsa kan ayyukan 'yan fashi da ke addabar al'umman yankin arewa maso yamma.
Ya soki fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Abubakar Ahmad Gumi da ya nemi gwamnatin tarayya da ta yi wa 'yan ta'addan, wadanda ke da alhakin mutuwar' yan Najeriya da dama da lalata dukiyoyi a fadin kasar afuwa.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hadimin shugaban kasa ya bayyana lokacin da Buhari zai karbi rigakafin korona
Gwamnan ya ce ya kamata Gumi ya yi wa masu laifin wa’azi kan illar kisan mutane ba nema masu afuwa ba, jaridar This Day ta ruwaito.
Masari ya sha alwashin cewa ba zai sake yin afuwa ga ‘yan fashi ba, yana mai cewa an ci amanar gwamnatinsa a shekarar 2016 da 2019 bayan sun bi ta wannan hanyar.
Ya ce mai laifi, mai laifi ne kuma babu abin da zai iya tabbatar da kisan 'yan kasa da ba su ji ba basu gani ba.
Ya kara da cewa:
"Duba abokina, ɓarawo, ɓarawo ne kuma mai aikata laifi, mai laifi ne. Suna da laifi kuma ba za su iya ba da hujjar kashe rayukan bayin Allah ba."
KU KARANTA KUMA: Zamfara na jiran ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan sojan da ke kai wa yan bindiga kayayyaki
A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki fitaccen malamin addini, Sheikh Ahamd Gumi a kan tsokacinsa, inda yace a ninke yake a cikin duhu.
Fani-Kayode yayi martani ne a kan tsokacin Gumi inda yace in har za a iya yafewa masu shirya juyin mulki, me zai sa ba za a iya yafewa 'yan binidga ba?
Fani-Kayode yace "Ta yuwu mu yiwa Hitler, Pol Pot, Stalin, King Leopard 11 na Belgium, Osama Bin Ladin, Al Bagdadi, Abubakar Shekau da duk wani wanda ya kashe mutane da yawa afuwa bayan mutuwarsu saboda tarihin da suka kafa a duniya."
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng